Home Back

Gwamnatin Tinubu Ba Za Ta Goyi Bayan Auren Jinsi Ba – Minista

leadership.ng 2024/10/5
Yajin aiki

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ba za ta goyi bayan duk wani yunƙuri na auren jinsi ko tarayyar ‘yan luwaɗi da maɗigo a Nijeriya ba.

Ministan ya bayyana haka ne a yayin da yake martani kan labarin da aka yaɗa a ranar Alhamis cewa Gwamnatin Tarayya ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya da aka yi a ƙasar Samoa, wadda za ta ba da dama a hukumance ga ‘yan luwaɗi da masu maɗigo a Nijeriya.

A rahoton da wasu kafafen yaɗa labarai suka buga, an ruwaito cewa, yarjejeniyar ta ƙunshi wasu tanade-tanade ne waɗanda ke buƙatar goyon bayan kare haƙƙin ‘yan luwaɗi da masu maɗigo a matsayin sharaɗin samun tallafin kuɗi da sauran taimako daga ƙasashen da suka ci gaba.

Lamarin dai ya haifar da ce-ce-ku-ce, inda wasu malaman addini da masu rajin kare haƙƙin ɗan Adam ke sukar gwamnati kan amincewa da yarjejeniyar da ta yi.

To amma a ƙarin hasken da ya yi kan yarjejeniyar, Minista Idris ya ce ai Nijeriya tana da dokoki tun tuni waɗanda suka haramta auren jinsi ko tarayyar ‘yan luwaɗi da masu maɗigo, kuma dokokin sun girmi wannan yarjejeniyar ta Samoa da ake ta ce-ce-ku-ce a kan ta.

Ya ce, “A ranar 28 ga Yuni, 2024 ne gwamnatin Nijeriya ta rattaba hannu kan yarjejeniyar Samoa ɗin a sakatariyar Ƙungiyar Ƙasashen Afirka, Karibbiyan da Pacific (OACPS) a birnin Brussels na ƙasar Beljiyam.

“An fara tattaunawa kan yarjejeniyar tun a shekarar 2018, a lokacin taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 73. Ɗaukacin ƙasashe membobin Tarayyar Turai su 27 da ƙasashe 47 daga cikin 79 na OACPS ne suka rattaba hannu kan yarjejeniyar a garin Apia da ke Tsibirin Samoa a ranar 15 ga Nuwamba, 2018.

“Nijeriya ta rattaba hannu kan yarjejeniyar ne a ranar Juma’a, 28 ga Yuni, 2024. Hakan ya biyo bayan nazarin da ta yi tare da tuntuɓar Kwamitin Ministoci da Ma’aikatar Kasafin Kuɗi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki ta kafa tare da haɗin gwiwar Ma’aikatar Harkokin Ƙasashen Waje da Ma’aikatar Shari’a ta Tarayya.

“An tabbatar da cewa babu ɗaya daga cikin Tanade-tanade 103 na yarjejeniyar waɗanda suka saɓa wa Kundin Tsarin Mulki na 1999 wanda aka yi wa kwaskwarima ko dokokin Nijeriya, da sauran wasu dokoki.

“Bugu da ƙari, amincewar da Nijeriya ta yi yana ƙunshe da sanarwa mai ɗauke da kwanan wata 26 ga Yuni, 2024, inda ta fayyace fahimtar ta da kuma yanayin yarjejeniyar a ƙarƙashin ikon ta na cewa ba a amince da duk wani tanadi da ya saɓa wa dokokin Nijeriya ba.

“Yana da kyau a lura da cewa akwai dokar da aka kafa a Nijeriya game da dangantakar auren jinsi ɗaya tun a cikin 2014.”

A ƙarshe, ministan ya ce, “Ya zama wajibi a tabbatar wa da ‘yan Nijeriya cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, kasancewar ta gwamnati mai bin ƙa’ida, ba za ta shiga wata yarjejeniya ta ƙasa da ƙasa wadda za ta cutar da ƙasa da ‘yan ƙasar ta ba.

“Yarjejeniyar Samoa ba komai ba ce illa wani muhimmin tsarin doka na haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen ƙungiyar OACPS da Tarayyar Turai don inganta cigaba mai ɗorewa, da yaƙi da sauyin yanayi da illolinsa, da samar da damar zuba jari, da samar da haɗin gwiwa tsakanin ƙasashe mambobin OACPS a matakin ƙasa da ƙasa.”

People are also reading