Home Back

Xi Jinping Ya Yi Shawarwari Da Takwaransa Na Kasar Kazakhstan

leadership.ng 3 days ago
Xi Jinping Ya Yi Shawarwari Da Takwaransa Na Kasar Kazakhstan

Da safiyar yau Laraba ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi shawarwari da takwaransa na kasar Kazakhstan Kassym-Jomart Tokayev, a birnin Astana fadar mulkin kasar.

Yayin ganawar ta su, Xi Jinping ya ce, an kafa zumunci tsakanin kasashen biyu bisa hanyar siliki mai tarihin fiye da shekaru dubu 1, kuma ya kai ga matsayin huldar abota bisa manyan tsare-tsare a duk fanonni mai dorewa bayan shekaru 32 da kullar dangantakar diplomasiyya tsakaninsu, hakan ya sa muhimman abubuwan dake cikin huldar kasashen biyu suka kunshi sada zumunta daga zuri’a zuwa zuri’a, da amincewa juna, da cin moriya da magance matsaloli tare.

Ban da wannan kuma, Xi Jinping ya jadadda cewa, Sin ba za ta sauya matsayin da ta dauka na kiyaye zumuncinsu, da ingiza hadin kansu a duk fannoni ba, da goyon bayan juna kan muradu masu tushe, da ma tabbatar da hadin gwiwar kasashen biyu a duk fannoni, duk da irin sauye-sauyen da duniya ke fuskanta.

A wannan rana kuma, Xi Jinping da Kassym-Jomart Tokayev sun halarci bikin kaddamar da cibiyar nune-nunen ala’dun kasashen Sin da Kazakhstan, da reshen Kazakhstan na jami’ar koyon harsuna ta Beijing. Kaza lika ta kafar bidiyo, sun halarci bikin kaddamar da hanyar sufurin kaya mai saurin tafiya da ta hada Sin da Turai wadda ta ratsa tekun Caspian. (Amina Xu)

People are also reading