Home Back

Ramadan: Wike Ya Raba Wa Musulmai Kayan Abinci A Abuja

leadership.ng 2024/5/6
Ramadan: Wike Ya Raba Wa Musulmai Kayan Abinci A Abuja

Ministan babban birnin tarayya, Abuja Nyesom Wike, ya raba wa Musulmai mazauna birnin kayan abinci albarkacin watan Ramadan.

Wadanda suka samu tallafin kayan abincin sun hada da masu sarautun gargajiya, masallatai, da kungiyoyin jin-kai, inda suka samu shinkafa, sukari, madara da sauran kayan masarufi.

Mista Samuel Atang wanda ya wakilci Wike, ya jaddada muhimmancin tallafa wa mazauna birnin a cikin watan Ramadan.

Ministan ya yi rabon ne da nufin rage tasirin tashin farashin kayayyakin abinci da kuma tabbatar da cewa musulmi sun yi buda baki cikin sauki.

Wike, ya bukaci al’ummar Musulmi su yi wa Nijeriya addu’ar samun zaman lafiya da kuma yi wa Shugaba Tinubu addu’a.

Daraktan tsare-tsare na birnin tarayya, Alhaji Sani Daura, ya bayyana kudirin gwamnati na tallafa wa mabukata a Abuja, don saukaka musu rayuwa a Ramadan.

An raba buhun shinkafa 5000, katan din mai 1000, katan-katan na sukari 1000, da kuma katan din madara 1000.

Wani limami, Ustaz Lawal Mustafa da Kwamared Bala Tsoho Musa, sun bayyana jin dadinsu da tallafin kayan abincin.

Sun bayyana cewar kayan abincin za su taimaka wa wadanda suka rabauta da su a wannan wata mai alfarma na Ramadan da ake ciki.

People are also reading