Home Back

Za Ka Ji a Jikinka": An Bayyana Jerin Kalaman Jonathan Ga Buhari Kafin Barin Mulki

legit.ng 2024/7/3
  • An gano abin da tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya fadawa Muhammadu Buhari lokacin da zai bar mulki
  • Jonathan ya fada cewa gwmnatin da za ta gaje shi za ta fuskanci matsaloli da dama marar misaltuwa
  • Bayan saukar Jonathan, tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ne ya gaji kujarar a shekarar 2015 har zuwa 2023

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya gargadi Muhammadu Buhari lokacin barin kujerar mulki.

Jonathan ya ce yana tausayin gwamnatin da za ta karbi mulki a wancan lokaci inda ya nuna damuwa kan halin da za su tsinci ƙasar.

Tsohon hadimin Jonathan, Doyin Okupe shi ya tabbatar da haka a cikin wani faifan bidiyon YouTube yayin hira da Channels TV.

Okupe ya ce mai gidansa ya yi hasashen halin da kasar za ta shiga tun a wancan lokaci yayin da zai bar mulki.

Tsohon hadimi ya ce Jonathan ya fada masa cewa gwamnatin da za ta karbi mulki za ta fuskanci matsaloli.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Lokacin da zamu bar mulki, ana saura kwanaki kadan mu bar ofishin mulki ina tare da Goodluck Jonathan a cikin wani yanayi."
"Na tambaye shi Oga lafiya kuwa? Sai ya ce yana tausayawa gwamnatin da za ta gaje shi."
"Ya ce za ta fuskanci matsaloli masu tarin yawa da kalubale."

- Doyin Okupe

Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari shi ne ya gaji kujerar Jonathan bayan kayar da shi a zaben 2015.

Daga bisani, Buhari ya sake tsayawa takara a zaben 2019 inda ya sake yin nasara kafin kammala wa'adinsa a shekarar 2023.

Buhari ya taya Tinubu murna

Kun ji cewa tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya taya Shugaba Bola Tinubu murnan cika shekara daya a kan mulki.

Buhari ya kuma bukaci ƴan Najeriya da su ci gaba da ba Tinubu goyon baya domin inganta rayuwar ƴan ƙasar.

Asali: Legit.ng

People are also reading