Home Back

...Daga Bakin Mai Ita tare da Bashir na Daɗin Kowa

bbc.com 2024/7/1

...Daga Bakin Mai Ita tare da Bashir na Daɗin Kowa

Minti 1 da ta wuce

A wannan makon mun kawo muku hira da Mudassir Abdullah Ibrahim, da aka fi sani da Bashir a cikin fitaccen film ɗin Daɗin Kowa da tashar Arewa24 ke shiryawa.

Matashin ɗan asalin jihar Borno - wanda ya girma a Kano - ya ce ya fara sha'awar harkar film ne tun yana ƙarami.

Ya ce tun yana shekara biyar ya bar jihar Borno, ya koma Kano, inda a nan ne ya yi komai nasa na rayuwa.

Bashir ya ce tun yana ƙarami shi da abokansa sukan karɓo hayar kyamara, su ɗauki film sannan su kalle shi suna nishadi.

Ya ƙara da cewa sanadiyyar film ya koyi mu'amala da mutane, sannan ya mu'amalanci mutanen da bai taɓa tunanin zai yi mu'amala da su ba.

Ya ce gwanayen jarumansa a Kannywood su hada da marigayi Ahmad S. Nuhu, da Ali Nuhu, sai a mata kuma Nafisa Abdullahi.

Jarumin ya ƙara da cewa fatan sa shi ne ya yi film da jarumi Ali Nuhu, domin shi ne tauraron masana'antar da ya ke nurin ya yi fim da shi.

Ya kuma ce babban burinsa a film shi ne, fatan gamawa lafiya.

People are also reading