Home Back

Dhul Hijjah: Saudiyya Ta Fitar da Sanarwa Kan Ranakun Arfah da Babbar Sallah

legit.ng 2024/7/7
  • Hukumomin ƙasa mai tsarki sun buƙaci Musulmai su fara duban jinjirin watan Dhul Hijjah idan Allah ya kaimu gobe Alhamis, 29 ga Dhul Qa'adah
  • A wata sanarwa da kotun ƙolin Saudiyyya ta fitar ranar Laraba, ta ce ganin watan zai tabbatar da ranakun aikin hajji da suka haɗa da Arfah da Babbar Sallah
  • A ranar 10 ga watan Dhul Hijjah Musulmi ke gudanar da Babbar Sallah, ɗaya daga cikin ibada masu muhimmanci a Addinin Musulunci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Saudi Arabia - Hukumomi a ƙasar Saudiyya sun buƙaci al'ummar musulmi na ƙasar su fara duba jinjirin watan Dhul Hijjah gobe Alhamis.

Watan Dhul Hijja wanda ya kasance wata na 12 a jerin kalandar addinin Musulunci, shi ne watan da Musulman duniya ke yin sallar layya.

Za a fara duban wata a Saudiyya.
Kotun kolin Saudiyya ta buƙaci a fara duban jinjirin watan Babbar Sallah daga gobe Alhamis Hoto: Inside Haramain Asali: Twitter

Ranar Alhamis, 6 ga watan Yunin 2024 za ta kasance daiɗai da 29 ga watan Dhul Ƙa'ada, bisa haka hukumomin Saudiyya suka nemi a fara duban watan 12.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotun ƙolin saudiyya ce ta bayyana haka a wata sanarwa da shafin Inside Haramain ya wallafa a manhajar X wadda aka fi sani da Twitter.

Sanarwan ta ce:

"Kotun koli na kira ga ɗaukacin Musulmin ƙasar Saudi Arabia su fara duban jinjirin watan Dhul Hijjah daga gobe Alhamis, 29 ga watan Dhul Qa'adah, 1445AH daidai da 6 ga watan Yunin 2024.

"Ganin jinjirin watan ne zai tabbatar da ranakun aikin hajji da ranar hawan Arfah da kuma ranar babbar Sallah."

Sanarwar ta buƙaci waɗanda za su iya duban watan da idanuwansu ko na'urar hangen nesa da su kai rahoton ganin watan ga kotu mafi kusa da su.

Musulmai na gudanar da idin Babbar Sallah ne ranar 10 ga watan Dhul Hijjah na kowace shekara, yayin da Alhazai ke hawan Arfah ranar 9 ga watan 12 a Musulunci.

Asali: Legit.ng

People are also reading