Home Back

Ciyarwar Ramadan: Gwamna Dauda Lawal, Talakawa na Bukatan a Agaza musu, Ka Tallafawa Talakawan Jihar Zamfara, Daga Imam Murtadha Gusau

premiumtimesng.com 2024/4/29
Ciyarwar Ramadan: Gwamna Dauda Lawal, Talakawa na Bukatan a Agaza musu, Ka Tallafawa Talakawan Jihar Zamfara, Daga Imam Murtadha Gusau

Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai

Assalamu Alaikum wa rahmatullah wa bara ka tuh

“Ya mai girma Gwamna, ina mai baka shawara, da ka zama mai yin sadaka, mai kyauta; ka ciyar da bayin Allah a wannan wata mai albarka, kayi alkhairi, sai ayi koyi da kai. Sanadiyyar haka sai Allah ya tausaya muna, ya saukar da rahamarsa a jihar mu mai albarka.” ~ Imam Murtadha Gusau

Ya ku bayin Allah! A gaskiya Al’amarin ciyarwa, da kyauta da sadaka a mahangar addinin Musulunci, ana iya cewa baiwa ce da Allah yake yiwa wasu daga cikin bayinsa, kuma Ibadah ce mai girman gaske, kuma muhimmiya. Bisa dalilin muhimmancinta yasa Allah Subhanahu wa ta’ala Yayi umurni da ciyarwa, yin kyauta da sadaka. A ɗaya ɓangaren, sai aka kwaɗaitar da yawaita ciyarwa, kyauta da sadaka, tare da bayyana dimbin fa’idojin da suke jawowa wanda yake yin su. Akwai ayoyin Alkur’ani mai girma masu yawa, waɗanda aka tsoratar da al’ummah yin rowa a cikinsu, tare da nuna illolin da rowa take jawo wa mai yinta, watau marowaci.

Bayan ayoyin Alkur’ani mai girma kuma, akwai Hadisan Manzon Allah (SAW) masu tarin yawa da suka nuna muhimmancin ciyarwa, sadaka da yin kyauta. A Musulunci an kira kyauta, ciyarwa da sadaka (wato bayarwa) da sunaye daban-daban kamar: zakkah da zakkatul fitir (zakkar kono) da infaƙi (ciyarwa) da waƙaf (bayar da gida ko gona ko makaranta) da wasiyyah da layyah da hadayah da sauransu.

Ciyarwa, kyauta da Sadaka suna da kusanci da juna matuƙa don sun yi kama, sau da yawa abin da yake bambanta su ita ce niyyah.

An umurci Musulmi da su zama masu kyauta, su ba da zakkah da sadaka da waƙafi. Dukkan waɗannan domin a kori ko a kawar da rowa a tsakanin al’ummar Musulmi, kuma a samu zaman lafiya, da kaunar juna, da ci gaba mai dorewa.

Saboda muhimmancin sadaka, ciyarwa da kyauta a Musulunci, an ambace su a wurare da dama a cikin Alkur’ani mai girma, kamar a Suratul Baƙara aya ta: 219, 270, 272, 274, 291, da Suratul Ali’imrana aya ta 92, 134, da Suratul Nisa’I aya ta 114, da Suratul Taubah aya ta 60, 79, 103, da Suratul Nur aya ta 56, da Suratul Mujadalah aya ta 12, 13.

Kuma an yi umurnin yin sadaka, da ciyarwa da bayar da kyauta a Suratul Baƙara aya ta 271.

Kuma an ambaci fa’idoji da falalar ciyarwa da sadaka a Suratul Baƙarah aya ta 261, da Suratul Anfal aya ta 60, da Suratul Hadid aya ta18, da Suratul Tagabun aya ta17.

Kuma Allah Subhanahu wa ta’ala ya tsoratar da bayinsa a kan ƙin ciyarwa, da kin yin sadaka, da kin yin kyauta a Suratul Isra’il aya ta 28, kai da dai ayoyi da surori masu tarin yawa a cikin AlƘur’ani mai girma, kamar:

Suratul Isra’il aya ta 29. A inda aka ce kar ka zama mai maƙe hannunka, wato ka zama marowaci, kar kuma ka zama almubazzari don kar ka zama abin zargi, ko ka talauce.

Da kuma a cikin Suratul Laili. Da Suratul Ma’un, da cikin Suratul Hadid.

Sannan Abu Hurairah ya ruwaito Annabi (SAW) yace:

“Mai ciyarwa da kyauta yana kusa da Allah, kuma yana kusa da Aljannah, kuma yana kusa da mutane. Amma marowaci kuwa yana nesa da Allah, kuma yana kusa da wuta. Kuma jahili wanda yake yin kyauta da ciyarwa yafi kusa da Allah fiye da mai Ibadah marowaci.” [Tirmizi ne ya ruwaito shi]

Aliyu Ɗan Abi Ɗalib yace:

“Malami saboda iliminsa yana iya zama mai kyauta. A inda mai dukiya saboda son dukiyarsa yana iya zama marowaci.”

Sannan a Musulunci, an fifita mai ciyarwa da bayar da kyauta a kan wanda yake sai dai ya karɓa. kamar wani Hadisi da yace:

“Hannun sama (Mai bayarwa) yafi hannun ƙasa (mai karba) daraja.”

‘Yan uwa masu girma! Duk wannan yana nuna muna kyawon ciyarwa da kyauta fiye da rowa da kuma kwaɗayi.

Ibn Abbas yace:

“Manzon Allah (SAW) shine mafi alheri (Kyauta) a mutane. Kuma yafi yin kyauta, sadaka da ciyarwa a watan azumi, domin yafi iska kyauta.”

Abdullahi Bin Amr yace, wani mutum ya tambayi Annabi (SAW) cewa:

“Wane aiki ne yafi a Musulunci? Sai yace ka ciyar da talaka, sannan kayi sallama ga wanda ka sani da wanda ba ka sani ba.” [Bukhari ne ya ruwaito shi]

Ya ku bayin Allah! Duk da wadannan bayanai, duk da wadannan nassoshi daga Allah da Manzonsa, to mu gaskiyar magana, a jihar Zamfara abun ba haka yake ba. A jihar Zamfara lamarin yasha banban. Domin Allah ya bamu wani irin gwamna, wanda shi a fahimtarsa, yana ganin cewa, a taimaki talakawa, a tallafawa bayin Allah, a ciyar da mutane, a fitar da dukiyar jiha, a baiwa ‘yan jihar, domin a rage masu radadin talauci da yunwa da damuwa da suke ciki, shi yana ganin wannan bata kudi ne a banza. Yana ganin wannan bannar dukiya ce.

Tun da watan Ramadan ya kama, a ko wace jiha daga cikin jihohin Najeriya, an raba wa talakawan jihar kayan arzuka da kudade da abinci iri-iri, domin rage masu radadin matsin rayuwar da suke ciki, domin kuma su samu damar yin Ibadar azumin watan Ramadan cikin walwala da annashuwa, amma Gwamnatin jihar Zamfara, karkashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal, shiru kake ji, wai an aiki bawa garin su.

Yau litinin, takwas ga watan Ramadan, amma gwamnatin jihar Zamfara, har zuwa yanzu bamu ji abunda tayi ba.

Irin yadda muke ji, kuma muke gani, Gwamnatocin wasu jihohi irin Kano, Borno, Jigawa, Sokoto, Kebbi da sauransu, suna ta kokarin taimakawa bayin Allah, suna ta rabon kayan rage radadin halin matsin rayuwa da ake ciki (wato palliatives), domin rage radadin damuwar da ake ciki, amma wallahi a jihar Zamfara babu wannan daga bangaren Gwamnati. To ko a boye take yi ne, ko a sirrance suke yi, to mu dai bamu sani ba?

A jihar Zamfara, in ban da aka samu wasu bayin Allah, wasu ‘yan siyasa, wasu masu hannu-da-shuni, masu jinkai da tausayi, suna kokartawa, da wallahi bamu san halin da talakawa zasu shiga ba a jihar.

Misali, ‘yan siyasa irin su tsohon Gwamnan jihar Zamfara, kuma Ministan Tsaro, Muhammad Bello Matawalle, da tsohon Gwamna, kuma Sanata mai ci, Alhaji Abdul’aziz Yari, da ‘yan siyasa irin su Honorabul Aminu Sanin Jaji, da irinsu Sarkin Dawaki mai tuta, da sauran ‘yan siyasa, da masu hannu da shuni, da suke ta kokari da hobbasa, wurin ganin an dan samu sa’ida, da wallahi bamu san halin da jihar za ta sake tsunduma ba na ni-‘ya-su, domin dai daga bangaren Gwamnati kam babu wani abu da muka ji ko muka gani.

Kai ko wuraren buda baki da aka saba budewa duk shekara a jihar Zamfara, domin bayin Allah su amfana, wanda wannan aiki an faro shi ne tun lokacin tsohon Gwamna, Ahmad Sani Yariman Bakura, a wannan gwamnati ta Dauda Lawal mu duk bamu ga wannan ba, komai ya tsaya cik.

Wadancan gwamnoni da na ambata a sama, wallahi duk sun bude wuraren buda-baki da ciyar da abinci a jihohinsu, bayan danyen abinci da suka raba wa talakawan su, saboda dimbin bayin Allah wadanda basu da abun buda-baki, wanda kuma mun san jihohin nan a can baya duk suna koyi ne da jihar Zamfara wurin maganar ciyarwa Ramadan, albarkacin tsohon gwamna, Ahmad Sani Yariman Bakura, amma a yau duk wannan ya kau.

Kuma wallahi, a wannan lokacin da muke ciki a yau, jihar mu ta Zamfara mai albarka, ba ta da matsalolin da suka wuce matsalar tsaro da matsalar yunwa da talauci. Mutane a jihar suna cikin matsananciyar yunwa, talauci da damuwa mai tarin yawa.

A yau, wallahi ba gine-ginen tituna ne matsalolin Zamfarawa ba. A jihar Zamfara ne fa mutane suke cin wasu ganyayyakin daji domin su rayu. Mutane suna faduwa suna mutuwa saboda tsananin yunwa. Amma duk da haka sai aki mayar da hankali wurin tallafawa al’ummah? Wane irin mulki ne wannan domin Allah?

Ya kamata wannan Gwamnati ta Dauda Lawal, da duk magoya bayan ta, su san da cewa, a Najeriya fa ana fama da halin matsin rayuwa. Don haka a halin yanzu wallahi, ka ciyar da mutane, ka tallafawa mutane, ka rage masu radadin matsin rayuwa, yafi kaje kana wani gine-ginen hanyoyi da tituna.

Meye amfanin ginin hanya ko titi, alhali mutane suna ta mutuwa da yunwa?

Haba jama’ah, me yasa ne ba zamu ji tsoron Allah, mu fada wa junan mu gaskiya ba?

Alfarmar wannan wata na Ramadan, wallahi har wani gwamna kirista a kasar nan ya tallafawa musulmi a jiharsa, to amma jihar da ake ikirarin ana aiwatar da Shari’ar Musulunci, nan ne za’a kalli ciyar da bayin Allah kamar wata hanyar barnar dukiya ga banza? Haba don Allah.

Maimakon gwamnatin jihar Zamfara ta sawo dimbin kayan abinci, a taimakawa al’ummah, kawai sai ta buge ga aika wa ma’aikatan jihar wani bonus na shirme, wanda bai taka-kara-ya-karya-ba. Bonus din da ba wani amfanin da zai yi masu.

Idan ma har wannan bonus zai amfanawa ma’aikata a jihar, to su wadanda basu aikin gwamnati fa, wane irin tallafi gwamnati za ta basu? Ko su ba ‘yan jihar bane?

Don Allah muna kira ga gwamnatin jihar Zamfara akan ta canza wannan tsari na ta, na matse hannu da matse bakin aljihu. Ya kamata Gwamna ya san da cewa, baitulmalin jihar Zamfara dukiyar ‘yan jihar ce, don haka ba laifi ne ba ya tallafa masu, ta hanyar ciyarwa, musamman a wannan wata mai albarka na Ramadan.

Kuma ai kamata yayi a rinka duba maslahar al’ummah, musamman ganin irin halin da ake ciki a yau. Fifita abun da mutane suke bukata a halin yanzu shine akan gaba. Yanzu abubuwan gaba-gaba da suke damun mutane, sune maganar tsaro da kuma halin hauhawar farashin kayayyakin masarufi, halin yunwa da karancin abinci, da sauransu.

Amma maganar gine-ginen hanyoyi da tituna, wannan ba shine al’ummah suka fi bukata ba a yau wallahi.

A bari tsaro ya samu mana, ayi kokari a kau da yunwa da talauci, sannan ayi maganar hanyoyi da tituna. Wannan shine gaskiyar magana.

Kai ma misali, ai wadancan jihohi, wadanda suke tallafawa talakawan jihohinsu, su ma suna yin hanyoyin da titunan da gine-ginen gadoji da sauransu, amma duk da haka, kuma suke tallafawa talakawan jihohin nasu.

Kun ga kenan ba hujja bace, kuma ba dalili bane, kawai ace don Gwamna yana yin hanyoyi da tituna, shike nan kuma ba zai ciyar da mabukata, bayin Allah, abincin Ramadan ba.

Don haka, muna kira ga Gwamna Dauda Lawal da ya gyara, domin amfanin kan sa da kuma amfanin al’ummar jihar Zamfara. Allah yasa a gyara, amin.

Sannan su ma kwamishinoninsa da ma’aikatansa da duk magoya bayansa, ya kamata su canza taku. Domin a jihar Zamfara anyi gwamnatota kafin tasu, amma duk ba haka suka tafiyar da gwamnatocinsu ba.

Kowa ya sani, idan watan Ramadan yazo da watan Sallah, duk ana tallafawa talakawa da mabukata da sauran al’ummar jiha da suke bukatar tallafi. Amma sai ga wannan gwamnati, duk da ita da ma’aikatanta, abubuwa duk sun yi shiru.

Tambaya anan shine. Shin Ku gwamnatinku haka take ne?

Ya kamata mu sani, taimakawa talakawa da ciyar da bayin Allah suna sanyaya fushin Allah, suna jawo wa al’ummah alkhairai masu tarin yawa.

Daga karshe, ina mai mika sakon ta’aziyya ta ga iyalai da dukkanin al’ummar jihar Zamfara baki daya, akan babban rashi da muka yi na babban malami, kuma baban mu, wato Sheikh Surajo Rabi’ah.

Ina addu’a da rokon Allah ya jikansa, Allah ya gafarta masa, Allah ya yafe kura-kurensa, Allah haskaka kabarinsa, Allah yayi masa sakamako da Jannatul-Firdausi, amin.

Wassalamu alaikum,

Dan uwanku: Imam Murtadha Muhammad Gusau, ya rubuto daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samun Imam ta wannan lambar waya kamar haka: 08038289761.

 
People are also reading