Home Back

Yadda tsananin zafi ke kashe mutum 100 a kullum a Pakistan

bbc.com 3 days ago
Lokacin da BBC ta kai ziyara asibitin Civil Hospital, kusan duk waɗanda suka kai akn su sashen kulawar gaggawa sun je saboda bugun zafi
Bayanan hoto, Lokacin da BBC ta kai ziyara asibitin Civil Hospital, kusan duk waɗanda suka kai kan su sashen kulawar gaggawa sun je saboda bugun zafi
  • Marubuci, Riaz Sohail
  • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Urdu

Da farar safiya, ana tsaka da tsananin zafi a Karachi mafi muni cikin shekara 10, direban babur mai ƙafa uku, Irshad Hussain mai shekara 54 ya fita daga gida domin fara aiki.

Sai dai kuma Irshad, wanda ke da lalura a zuciyarsa, ya faɗi saboda rashin lafiya a yankin Landhi na birnin har ma ya kasa tafiya.

Daga baya matarsa Sahabana Bano ta ji kira a waya daga ofishin 'yansanda cewa mijinta ya rasu.

A maƙabartar Edhi inda ta je domin karɓar gawar mijin nata, ta ce: "Muna zaune a gidanmu a wannan lokacin na zafi.

"Amma yanzu magidancin ya tafi har abada, inda ya bar 'ya'ya mata biyar da namiji ɗaya."

Tsananin zafin ya kuma yi sanadiyyar kashe wani matashi mai shekara 25 mai suna Liaquat, wani ɗandako a kasuwar tifafi ta Khara Dar - yana tsaka da lodin kaya katsam sai ya faɗi a sume.

Tun daga ƙarfe 11 na safe ma'aikata a kasuwar ke fara fama da tsananin gumi.

Suma a titunan Karachi

Direbobin motar marasa lafiya kamar Shabir Zaman na fama da tsananin zafin su ma a Karachi
Bayanan hoto, Direbobin motar marasa lafiya kamar Shabir Zaman na fama da tsananin zafin su ma a Karachi

Pakistan ta yi ta fuskantar tsananin zafi tun daga watan Mayu, inda ya dinga wuce 50C a ma'aunin zafi a wasu yankunan ƙasar.

A Karachi - birnin kasauwancin ƙasar - miliyoyin mutane ne ke kaiwa da kawowa a tituna kuma da yawa na fuskantar mnatsala.

Shabir Zaman, wani direban motar marasa lafiya ta ƙungiyar Edhi, ya bayyana yadda ya ɗauki wani matashi zuwa asibiti bayan ya faɗi yana tsaka da aiki.

Ma'aikacin Gidauniyar Edhi mai suna Muhammad Nadeem ya faɗa wa BBC ya kai mutum takwas da suka suma asibiti daga yankunan Bahadurabad, da Tariq Road, da maƙwabtansu saboda tsananin zafin.

Ɗakunan ajiyar gawa sun cika maƙil

Gawar mutanen da suka mutu a Karachi saboda tsananin zafi na cika ɗakunan ajiyar gawawwaki
Bayanan hoto, Gawar mutanen da suka mutu a Karachi saboda tsananin zafi na cika ɗakunan ajiyar gawawwaki

An fara ba da rahotonnin tsananin zafi a Karachi ne lokacin da shugaban gidauniyar Faisal Edhi ya bayyana ƙaruwar gawawwakin da ake kaiwa ɗakunan ajiyar gawarsa uku.

A cewarsa, akan gawar mutum kusan 30 a kullum idan zafin bai tsananta da yawa ba, da kuma jimillar mutum 150 cikin kwana uku.

Idan kuma ya tsananta sosai, akan samu gawar mutum sama da 100 a kullum.

Ihtmamul Haq Thanvi, shugaban mutuwaren Masjid Trust, ya faɗa wa BBC cewa yawan gawar mutanen da ake kaiwa duk rana sun ƙaru a kwanan nan zuwa 25 ko 30 a kullum idan aka kwatanta da 12 zuwa 15 da aka saba samu.

Mista Edhi ya ƙara da cewa akasarin mutanen da suka mutu ma'aikata ne ko kuma masu ƙaramin ƙarfi da suka fito daga yankunan da ake yawan ɗauke wutar lantarki.

Sai dai akwai saɓani a yawan adadin mutanen da ke mutuwa saboda tsananin zafi a Karachi.

Kwamashinan birnin mai suna Karachi Syed Navi ya yi iƙirari a ranar Laraba cewa mutum 10 ne aka tabbatar sun mutu saboda tsananin zafin ya zuwa ranar 24 ga watan Yuni.

Ya kuma ce babu tabbas kan dalilin mutuwar mutanen da ake kaiwa mutuware.

A gefe guda kuma, alƙaluman da asibitin Civil Hospital suka bayar kaɗai sun nuna cewa mutum 15 ne suka mutu sannan wasu 360 ke samun kulawa daga 23 zuwa 27 ga watan Yuni.

Cunkoso a asibitoci

Marasa lafiya da yawa da aka kai asibitin Karachi na buƙatar na'urar taimaka wa nimfashi kafin su farfaɗo
Bayanan hoto, Marasa lafiya da yawa da aka kai asibitin Karachi na buƙatar na'urar taimaka wa nimfashi kafin su farfaɗo

Lokacin da BBC ta kai ziyara asibitin Civil Hospital, kusan duka waɗanda suka je asibitin na fama ne da lalurar bugun zafi.

A ɓangaren maza, akwai marasa lafiya biyu a kan kowane gado, da yawa daga cikinsu sanye da takunkumin nimfashi, inda likitoci da ma'aikan jinya ke yunƙurin bai wa kowa kulawa.

Imran Sarwar, likitan da ke kula da ayyuka, ya faɗa nana cewa ana kuma ba da rahoton gudawa da kuma ciwon ciki.

Zahida Khatoon na cikin waɗanda ke zaune a kan benci da kuma wata mace kwance a kan cinyarta.

Ta ce matashiyar da ke kwance sirikarta ce, wadda aka ɗaura wa aure kwana 11 da suka wuce lokacin da ta fara jin bugun zafi kuma ta fara amai kafin a kawo ta asibiti.

Direban motar marasa lafiya Shabir Zaman ya ce da yawa daga cikin abokan aikinsa ma sun faɗi saboda tsananin zafin.

"Idan ina cikin gida sai in ji kamar zuciyata za ta buga, zafin ya yi yawan da ba za a jurewa ba," a cewarsa.

Koyon darasi kan tsananin zafi

Mazauna Karachi a Pakistan

Birnin na Karachi ya koyi darasi daga tsananin zafin na 2015, lokacin da asibitoci suka daina karɓar marasa lafiya kuma mutuware suka cika.

An gina wasu ɗakunan ajiye gawa.

Ita kuma gidauniyar Edhi ta samar da wasu wurare biyu da za a iya ajiye gawar mutum biyu kan kowace kanta, amma kuma uku ake sakawa saboda yawan mutanen.

Wani darasin da aka koya daga 2015 shi ne ba a wayar da kan mutane sosai ba kan dalilin da ya sa zafin ke kashe mutane.

Amma kuma yanzu mutane sun gane yadda za su dinga kare kan su, kuma akwai sababbin wuraren kula da mutanen.

Misali, akwai sansanin kula da bugun zafi na gudaniyar Edhi, inda ake samar da ruwan sha kuma ake fesa wa mutane ruwa.

Direba Shabir Zaman ya ƙara da cewa: “Yanzu muna shan ruwa a ko'ina, duk inda muka ɗauki maras lafiya ko muka ajiye shi, za mu sha lemon zaƙi sannan mu dinga shan ruwa iya shanmu."

Abokin aikinsa Muhammad Nadeem ya ce kwaɗayin taimaka wa mutane ne kawai yake ƙara masa ƙwarin gwiwa.

People are also reading