Gane Mini Hanya
A Najeriya a na ci gaba da bayyana ce-ce-ku-ce game da yadda wasu 'yan siyasa da wasu fitattun ma'aikan gwamnati ke karɓar albashi da alawus-alawus da kuɗin sallama mai tsoka, a yayin da na wasu kuma bai taka-kara-ya-karya ba.
Inda Albashi da kuɗin sallama na shugaban ƙasa bai kai rabin na wani ma'aikaci a wata ma'aikata a ƙasar ba.
Abdussalam Ibrahim Ahmed ya tattauna da Muhammad Bello Shehu, shugaban hukumar tattara kuɗaɗe na gwamnatin ƙasar da rarraba su ga gwamnatin tarayya, da na jihohi da ƙananan hukumomi
Ga kuma ƙarin bayanin da ya yi.