Home Back

Hajji 2024: Wani Alhaji Daga Najeriya Ya Sake Rasuwa a Makkah

legit.ng 2024/7/2
  • Allah ya yiwa wani Alhaji da ya fito daga jihar Kebbi rasuwa a birnin Makkah yayin gudanar da aikin Hajjin bana na shekarar 2024 a ƙasa mai tsarki
  • Hukumar jin dadin Alhazan jihar wacce ta tabbatar da rasuwar Alhajin a cikin wata sanarwa ta ce ya fito ne daga Gulma cikin ƙaramar hukumar Argungu ta jihar
  • Shugaban hukumar a cikin sanarwar ya bayyana cewa marigayin ya rasu ne bayan ƴar gajeruwar lafiya kuma tuni aka yi jana'izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Saudiyya - Hukumar jin daɗin Alhazai ta jihar Kebbi ta sanar da rasuwar wani Alhaji a birnin Makkah na ƙasar Saudiyya.

Tawagar masu yaɗa labaran aikin Hajjin 2024 na jihar Kebbi suka bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi.

Wani Alhaji daga Kebbi ya rasu a Makkah
Wani Alhaji daga jihar Kebbi ya sake rasuwa a Makkah Hoto: Ashraf Amra/Anadolu Agency Asali: Getty Images

Alhaji daga Kebbi ya rasu a Makkah

Sanarwar ta ruwaito shugaban hukumar Alhaji Faruku Aliyu-Enabo yana tabbatar da rasuwar a birnin Makkah ranar Lahadi, cewar rahoton jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alhaji Faruku Aliyu-Enabo, wanda ya bayyana sunan marigayin a matsayin Abubakar Abdullahi daga Gulma a ƙaramar hukumar Argungu ta jihar, ya ce marigayin ya rasu ne bayan gajeruwar rashin lafiya.

Marigayin shi ne na uku daga cikin Alhazan jihar Kebbi da suka rasu yayin gudanar da aikin Hajjin bana a Saudiyya, rahoton jaridar PM News ya tabbatar.

Gwamna Nasir ya yi ta'aziyya

Ya ce Gwamna Nasir Idris ya bayyana kaɗuwarsa da rasuwar, inda ya kuma yi addu’ar Allah ya gafarta masa kurakuransa, ya sanya shi a Aljannatul Firdaus.

Ya ƙara da cewa gwamnan ya kuma buƙaci iyalan mamacin, abokansa da Alhazan jihar Kebbi da su yi haƙuri tare da ɗaukar dangana bisa wannan rashin da aka yi.

Shugaban ya bayyana cewa tuni aka yi jana’izar marigayin kamar yadda addinin Musulunci ya tanada bayan sallar jana’izarsa a masallacin Harami (Ka’aba) a ranar Juma’a.

Wata Hajiya ta rasu a Saudiyya

A wani labarin kuma, kun ji cewa wata Hajiya daga jihar Neja mai suna Ramatu Abubakar ta riga mu gidan gaskiya a ƙasa mai tsarki.

Hajiyar mai suna Ramatu Abubakar mai shekara 45 a duniya ta rasu ne a birnin Madina bayan ta kamu da rashin lafiya daga isarsu ƙasar Saudiyya.

Asali: Legit.ng

People are also reading