Home Back

Fitacciyar Jarumar Kannywood Saratu Giɗaɗo (Daso) ta rasu

dalafmkano.com 2024/5/14

Fitacciyar Jaruma a masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood Saratu Gidaɗo wadda akafi sani da Daso, ta rasu a yau Talata.

Mijin ƙanwar marigayiya Daso, kuma mai baiwa gwamnan Kano shawara a kan harkokin tafiye-tafiye da shaƙatawa Mustapha Ibrahim Chidari, ne ya tabbatar wa wakilinmu Bashir Sharfaɗi rasuwar ta a ranar Talata.

Ya ce da Asubar yau tayi Sahur, ta koma Bacci, sai dai kuma zuwa wajen ƙarfe 10 na safe aka ga bata fito daga ɗakin ta ba, ko da aka shiga ɗakin ne aka tarar ta rasu.

Mustapha, ya ce za’a yi jana’izar ta da yammacin Talatar nan, da misalin ƙarfe 04:30 a gidanta dake Chiranchi cikin garin Kano.

Marigayiya Daso, guda ce daga cikin fitattun jarumai a masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, wadda ta shafe shekaru a masana’antar.

People are also reading