Home Back

Gwamnatin Tinubu da Ƴan Kwadago Sun Gama Taron Gaggawa Kan Mafi Ƙarancin Albashi

legit.ng 2024/7/5

FCT Abuja - Rahotanni sun bayyana cewa an ƙarkare taron gaggawa da gwamnatin tarayya ta kira ƴan kwadago kan yajin aikin da aka fara yau.

Idan baku manta ba muna kawo rahoton cewa shugabannin ƴan kwadago sun isa ofishin sakataren gwamnatin tarayya domin shiga taron gaggawa da aka gayyace su.

Bola Tinubu da NLC.
An gama taron gaggawa tsakanin gwamnatin tarayya da yan kwadago Hoto: @aonanuga1956 Asali: Twitter

TVC News ta kawo cewa a halin yanzun gwamnati da ƴan kwadago sun ƙarkare taron na yau Litinin 3 ga watan Yuni, 2024.

Sai dai har kawo yanzu ƴan jarida na jiran bayanai daga ɓangarorin da suka halarci zaman, wanda aka shirya da nufin kawo ƙarshen yajin aikin ma'aikata.

Ku saurari ƙarin bayani...

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

People are also reading