Home Back

Ya Kamata Iran Da Isra’ila Su Kai Zuciya Nesa – Gwamnatin Nijeriya

leadership.ng 2024/5/18
Tinubu Ya Nemi Jihohi Su Dakatar Da Karbar Haraji A Kan Masu Safarar Kayan Abinci

Gwamnatin Nijeriya ta bi sahun sauran kasashen duniya wajen yin kira da a kai zuciya nesa kan barazanar Iran da Isra’ila.

Ta bukaci a ci gaba da tattaunawar diflomasiyya don ganin an kwantar da hankula da kuma kaucewa yaduwar rikici a yankin gabas ta tsakiya.

Wata sanarwa da ma’aikatar harkokin waje, ta fitar a ranar Lahadi, ta yi kira ga kasashen da su duba batun warware rikici cikin lumana.

Ta ce akwai bukatar samar da zaman lafiya da kuma tsaro a duniya baki-daya.

Hakan na zuwa ne bayan da Iran ta kaddamar da hari kan Isra’ila a daren Asabar, inda ta ce harin nata a matsayin ramuwa ne na kisan wasu kwamandojinta da Isra’ila ta yi a wani hari da ta kai karamin ofishin jakadancin ƙasar a Siriya, ranar 1 ga watan Afrilu, 2024.

Sai dai harin ya bar baya da kura, inda manyan kasashen duniya suka nuna rashin jin dadinsu game da matakin na Iran

People are also reading