Home Back

Makomar Matthijs de Ligt, da Branthwaite, da Keira Walsh

bbc.com 2024/7/6

Asalin hoton, Getty Images

.
Bayanan hoto, Matthijs de Ligt

Manchester United ta fara tattaunawar cikin gida kan mai tsaron baya na Netherlands da ke taka leda a Bayern Munich Matthijs de Ligt, dan shekara 24, wanda kulub din na Jamus ya taya a kan yuro miliyan 50. (Sky Sport Germany via TZ)

Manchester United ba ta da niyyar biyan fam miliyan 70 kamar yadda Everton ta bukata kan mai tsaron baya na Ingila, Jarrad Branthwaite, 21, sannan kuma ta yi barazanar ficewa daga tattaunawa kan sayan dan wasan. Tun da fari ta yi tayin fam miliyan 43 wadda a kai watsi da ita.(Mirror)

Arsenal na son dan wasan tsakiya na Ingila mai taka leda a Barcelona Keira Walsh, mai shekara 22. (Athletic - subscription required)

Valencia ta yi tayin fam miliyan 25, kan mai kai hari na Manchester United Mason Greenwood, mai shekara 22, ana rade-radin Juventus na son dan wasan Ingilar na gaba, amma da alama ya fi son zama a Sifaniya. (Mirror)

AC Milan na son Armando Broja, 22, na Albania, sai dai ana kyautata zaton zai ci gaba da taka leda a Chelsea. (Sky Sports Italy)

Manchester City na son yi wa Real Madrid dan waken zagaye, kan matashin dan wasan River Plate, na tsakiyar Argentina Franco Mastantuono, mai shekara 16, wanda ke kasuwa. (Sport, via 90 Min)

A baya-bayan nan Liverpool ta yi tuntuba kan dan wasan Stuttgart Waldemar Anton, mai shekara 27, wanda ke cikin tawagar Euro 2024, kan farashin fam miliyan 19 (Sport Bild - in German)

Juventus ta sha gaban Borussia Dortmund a kokarin dauko dan wasan Manchester United Jadon Sancho, mai shekara 24, wanda ya kare rabin kakar da ta wuce a kulub din Jamus. (Football Insider)

People are also reading