Home Back

Murna Yayin da Farashin Dala Ya Ƙara Karyewa a Kasuwar Hada Hadar Kudi a Najeriya

legit.ng 2024/9/28
  • Ƙimar Naira ta ƙara sama a kasuwar hada-hadar gwamnati ranar Talata sa'o'i 24 bayan kuɗin Najeriya sun rikita Dalar Amurka
  • Rahoton FMDQ ya nuna cewa Naira ta tashi da N3.31 inda aka yi musayar kowace Dalar Amurka kan N1,465.68
  • Shugaban kungiyar ƴan kasuwar cinikayyar kudi, Aminu Gwadabe, ya yabawa CBN da sauran hukumomin tsaro bisa matakan da suka ɗauka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Ga dukkan alamu Naira ta ƙara yunƙurowa a kasuwar hada-hadar kudi a lokacin da Dalar Amurka ke ƙara karyewa.

A ranar Talata, 21 ga watan Mayu, Naira ta farfaɗo da N3.31 a kasuwar gwamnati inda aka yi musayar kuɗi kan farashin N1,465.68/$.

Naira da Dala.
Darajar Naira ta ƙaru a kasuwar gwamnati ranar Talata Hoto: Contributor Asali: Getty Images

Bayanai daga hukumar kula da musayar kuɗi FMDQ sun nuna cewa ƙimar Naira ta ƙaru da kaso 0.22% a kasuwa idan aka kwatanta da farashin ranar Litinin, The Nation ta ruwaito

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Legit Hausa ta tattaro muku cewa a ranar Litinin, 20 ga watan Mayu, farashin Dalar Amurka ya karye zuwa N1,468.99.

Bugu da ƙari, an samu ƙarin yawan Dalolin da aka yi hada-hadarsu ranar Talata, inda adadin ya ƙaru zuwa Dala miliyan 268.17 daga $161.41m da aka yi cinikayyar su ranar Litinin.

Ana ganin dai hakan na da alaƙa da matakan da babban bankin Najeriya (CBN) ke ci gava da ɗauka domin dadaita kasuwar musayar kuɗi a Najeriya.

Kungiyar ƴan canji ta Najeriya (ABCON) ta yabawa CBN bisa tsare-tsaren da ya kawo wanda ke ƙara wa Naira daraja a kasuwar gwamnati, rahoton Vanguard.

Shugaban ABCON, Aminu Gwadabe, ya bukaci CBN ya ci gaba da aiwatar da irin waɗannan tsare tsare-tsaren da za su ɗaga ƙimar kuɗin mu na gida Najeriya.

Gwadabe ya alaƙanta fargaɗowar Naira da kokarin da gwamnati ke yi da kuma matakan da wasu hukumomin tsaro suka ɗauka.

"Ina farin cikin yadda hukumomi da dama suka haɗu domin tunkarar wannan ƙalubale," in ji Gwadabe.

CBN ya soke harajin yanar gizo

A wani rahoton kun ji cewa babban bankin Najeriya CBN ya kara kuɗin ruwa daga 24.75% zuwa 26.25% wanda ya kasance kari na uku kenan a cikin wannan shekara

Hakan na zuwa ne bayan soke biyan harajin yanar gizo da bankin ya yi niyyar ƙaƙabawa ƴan Najeriya bayan korafe-korafe da ake ta yi a kasar.

Asali: Legit.ng

People are also reading