Home Back

‘Yan Nijeriya Sun Fusata Da Kalaman Minista Kan Karin Kudin Wuta

leadership.ng 2024/5/20
wuta

Zafafan martani sun biyo bayan kalamun ministan wutar lantarki, Adebayo Adebalubu da ya ce za a fuskanci matsalar rashin wuta da shiga cikin duhu a fadin kasar nan da watanni uku muddin in aka ki amincewa da aiwatar da sabon karin kudin wutar lantarki.

Adelabu ya shaida hakan a lokacin da ya bayyana a gaban kwamitin majalisar dattawa kan wutar lantarki, da suke bincike kan karin kudin wuta da hukumar ku-la da wutar lantarki ta kasa (NERC) ta yi.
Wannan na zuwa ne bayan da kwamitin majalisar ya ki amincewa da karin kudin wutar lantarki a karkashin jagorancin, Sanata Enyinnaya Abaribe.

“Gabaki daya za a samu daukewar wutar lantarki muddin ba a kara kudin wuta ba. Daga nan zuwa watanni uku, Nijeriya za ta tsunduma cikin duhu muddin ba a kara farashin kudin wuta ba.
“Karin shi ne zai ba mu dama mu je mataki na gaba. Mu ma fa ‘yan Nijeriya ne, muna jin dukkanin zafin da kowa ke ji,” Adelabu ya shaida.

Sai dai kuma ‘yan Nijeriya sun nuna matukar fusatarsu da nuna damuwa kan wadannan kamalaman ministan, inda suka nuna cewa sam ba su tsammaci irin wadannan kalaman daga gareshi ba.
Owuru Odun-Itan Emmanuel ya ce, “Gwamnati ce da kanta ke jagorantar kuntata wa al’ummarta, ta jefa su cikin matsi da wahalhalun rayuwa.”

Abdulrahman Zubairu cewa ya yi: “Tinubu da ministocinsa sun ba mu kunya. Mun tafka babban kuskure na zabinsu. Muna addu’ar Allah ya ba mu dama mu canza su a nan gaba.”

Oyeyemi Olugbami y ace, “Wannan shi ne ke son mulkan jihata? Wai me ye sa ne a wannan gwamnatin komai sai kara kudi kawai yake yi, komai sai an kara masa farashi? Ba a saukaka wa talakawa ko kadan.”
Ahmad Shehu y ace, “A kowani lokaci kudin wuta karuwa kawai yake yi a kasar nan kuma bai yi tsayuwar da masu zuba hannun jari za su ji sha’awar zuba han-nun jarinsu ba, illa jefa ‘yan Nijeriya cikin wahala da ukuba. Gabaki daya komai ya lalacewa a tsarin harkar wuta. A kowani lokaci a cikin duhu ‘yan Nijeriya suke. Ban taba ganin ministan wuta marar amfani kamar wannan mutumin ba.

Muhammad Nasir Jabaka y ace, “Irin wannan ministan ne zai sa na yi addu’ar Allah ya kawo juyin mulki a wannan kasar, wannan gwamnatin ta yi watsi da muradin al’umman kasarta.”

People are also reading