Home Back

Shugaban Ƙasar Liberia Joseph Boakai Ya Rage Albashinsa da Kashi 40%

leadership.ng 2024/8/22
Shugaban Ƙasar Liberia Joseph Boakai Ya Rage Albashinsa da Kashi 40%

Shugaban ƙasar Liberia, Joseph Boakai, ya sanar da rage albashinsa na shekara da kashi 40% daga $13,400 zuwa $8,000. Wannan shawara ta zo ne a lokacin da jama’a ke kara matsa lamba kan albashin gwamnati da kuma yawan fushin talakawa game da tsadar rayuwa, inda kimanin kashi 20% na al’ummar ƙasar ke rayuwa a ƙasa da $2 a rana. Ofishin Shugaba Boakai ya bayyana cewa yana fatan kafa misali na shugabanci nagari da kuma nuna jituwa da al’ummar Liberia.

Sai dai kuma ra’ayoyi game da rage albashin sun sha bamban. Yayin da wasu ke yabawa da wannan mataki, wasu kuwa suna tambayar muhimmancinsa ganin cewa shugaban na ci gaba da karɓar wasu alawus-alawus da kuma kula da lafiyarsa.

Anderson D. Miamen na Cibiyar Gaskiya da Rikon Amana a Liberia ya kira matakin da cewa “mai kyau,” yayin da W. Lawrence Yealue II, wanda ƙungiyarsa ke fafutukar ganin gaskiya a cikin gwamnatin, ya bayyana matakin a matsayin “abin yabawa.”

Shugaba Boakai ya kuma ƙuduri aniyar ƙarfafa hukumar kula da ayyukan Jama’a ta Liberia don tabbatar da biyan albashi na adalci ga ma’aikatan gwamnati. Tun lokacin da ya hau karagar mulki a watan Janairu, ya ba da fifiko wajen yaƙi da cin hanci da rashawa da kuma rashin darajar kuɗin ƙasar, ya bayyana kadarorinsa, sannan ya ba da umarnin gudanar da bincike kan ofishin shugaban ƙasa.

People are also reading