Yadda Za Ku Warware Mas’alolin Sallar Idi Masu Rikitarwa, Sheikh Gidado Abdullahi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Sallar Idi sallah ce da ta bambanta da sauran sallolin da al'ummar musulmi su ka saba gudanar wa yau da kullum
Saboda haka ake yawan samun rudani a tsakanin masallata wanda warware su yakan bada wahala.
Sheikh Gidado Abdullahi, wani Malamin addinin a jihar Gombe ya warware manya daga cikin mas'alolin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Malamin addinin musuluncin ya warware mas'a'olin ne a shafin shi na Facebook, inda yake cewa:
Idan mutum ya samu liman yana karatun tahiya, zai zauna su yi karatun tare da liman, amma idan liman ya sallame zai tashi ya kawo raka'a biyu a siffar sallar Idi.
Idan kuma mutum ya samu liman ya kammala kabbori har ya fara karatu, zai fara da kabborin, idan ya gama kabborin sai ya saurari karatun liman.
Wani lokaci kuma mutum zai iya samun liman yana tsakiyar kabbarori, a wannan yanayin zai bi liman su karasa kabbarorin tare.
Bayan liman ya gama, sai ya kawo kabbarorin da suka wuce shi ko da liman ya fara karatu.
Idan kuma mutum ya samu liman yayi ruku'u, zai yi kabbarar harama ne kawai ya bi liman. A wannan yanayin babu bukatar kabbarori.
Babban malamin ya ja hankalin al'umma a kan muhimmancin sallar Idi da matsayinta a addini.
Shehin yana cewa saboda muhimmancin sallar ne Ma'aikin Allah –Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- ya bada umarni a rika yinta.
Ya kara da cewa saboda muhimmancin sallar ne ma ake bawa ma'aikata hutu domin su samu halartar ta.
Sheikh Gidado ya bayyana cewe Shari'a ta halastawa kowa zuwa sallar Idi. Maza da mata da kananan yara, har mata marasa tsarki idan sun je sai su yi nesa da wurin sallah.
Malamin ya ja hankalin iyaye akan su kula da sutura da mata da yara zasu saka yayin halartar sallar.
A cewar shi, bai kamata a barsu suna yin shiga data sabawa koyarwar addini ba.
Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Abubakar Sa'ad na III, ya bada sanarwar cewa gobe Laraba ne za'a yi sallar Idi a fadin Najeriya.
Sanarwar tazo ne bayan rashin ganin watan Shawwal a yammacin Litinin, hakan kuma yana nufin azumi talatin za'ayi bana.
Asali: Legit.ng