Home Back

TSADAR RAYUWA: Jigon APC ya ba Tinubu laƙanin gyara kurakuran da ya tsunduma Ƴan Najeriya cikin tsomomuwa

premiumtimesng.com 2024/4/29
TSADAR RAYUWA: Jigon APC ya ba Tinubu laƙanin gyara kurakuran da ya tsunduma Ƴan Najeriya cikin tsomomuwa

Jigon APC, Edet Nkpubre, ya bayyana waɗansu laƙanoni da ya ce ya ke so Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ɗauka, domin ya ceto tattalin arzikin Najeriya, tare da tsamo ‘yan Najeriya daga raɗadin tsadar rayuwar da ya jefa su a ciki.

Daga cikin shawarwarin da ya bayar, har da kafa dokar-ta-ɓaci kan dukkan muhimman sassa da ɓangarorin tafiyar da ƙasa.

Nkpubre, wanda tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar PDP ne na Kudu maso Kudu, wanda ya koma APC cikin shekarar da ta gabata, ya rubuta wa Shugaba Tinubu buɗaɗɗiyar wasiƙar, wadda aka riƙa yamaɗiɗi da ita a soshiyal midiya.

A cikin wasiƙar, Nkpubre ya ce raɗaɗin tsadar rayuwa, yawan tashin gwauron zabin da farashin kayan masarufi da kayan abinci ke yi, da kuma yunwa da ɓacin rayukan jama’a, “abubuwa ne tamkar bam ne aka ɗana, wanda aka saita lokacin tashin sa. Idan lokacin kuwa ya yi, to sai dai a ji ya tashi daram.”

Nkpubre ya shaida wa PREMIUM TIMES a ranar Lahadi cewa, shi ne da kan sa ya rubuta ta.

“Alamomin tsunduma cikin mummunan rikici sai ƙara bayyana su ke yi a ƙasar nan. Lamarin fa akwai firgitarwa.

“Abin da wannan masifar za ta iya haifar wa nan gaba ba zai zo wa ƙasar nan da daɗi ba.”

Saboda haka, ya kamata ka gyara kurakuran da ka tafka a farkon hawa mulkin ka. Kuma ka gaggauta kawo ƙarshen wannan masifa, gudun kada ta kai “matakan da za su hana ɓarkewar mummunar zanga-zanga a faɗin ƙasar nan.

Ya ce gaggawar cire tallafin fetur da Tinubu ya yi a a farkon hawan sa, ta na cikin abin da ya jefa ƙasar nan cikin masifar raɗaɗin tsadar rayuwa.

“Maganar kuɗin wutar lantarki kuwa, cewa ya yi ai duk duniya ko manyan ƙasashen da suka ci gaba ‘yan kasar kan samu wutar lantarki cikin rangwame, saboda gwamnatin ƙasar ke ciyar masu tallafin wutar lantarki.

 
People are also reading