Home Back

CharterHouse Lagos: Makarantar Firamaren da Ake Biyan Naira Miliyan 42 a Shekara

legit.ng 2024/5/2
  • Charterhouse Lagos, ƙasaitacciyar makarantar Firamare a jihar Legas da ake biyan Naira miliyan 42 duk shekara ta jawo cece-kuce tsakanin 'yan Najeriya
  • Cece-kucen ya samo asali bayan bayyanar kudin sayan fom din makarantar da aka ce ya kai naira miliyan 2
  • Wani kwararre kan al'amuran gudanarwa, Dr Dípò Awójídé ya ce irin wadannan makarantu kaso 1 cikin al'umma ne ke iya kai 'ya'yansu

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Legas - Makarantar firamare ta Charterhouse Legas ta zo da wani sabon salo inda ta sanya kuɗin nuna sha'awar shiga makarantar akan naira miliyan biyu.

Tuni hamshakiyar makarantar ta fara rajistar dalibai a zangon karatu na 2024/25, kamar yadda Legit ta ruwaito.

ChatterHouse Lagos
Dakin karatu bangaren firamare na makarantar ChatterHouse Lagos Hoto:charterhouselagos.com Asali: UGC

A bayanan dake shafin yanar gizon makarantar, ana bukatar iyayen da ke da sha'awar yaransu su shiga makarantar su cike takardar neman shiga, sannan su biya Naira miliyan biyu lakadan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

N42m kudin firamaren Charterhouse

Za a biya wa daliban da suka samu nasarar shiga kudin makaranta Naira miliyan 42 ko kuma Naira miliyan 31.5 ga wadanda aka bude makarantar da su.

Wannan na nufin za su samu ragin wuri na gugar wuri har na Naira miliyan goma.

A cewar wata mai amfani da shafin X, SisiYėmmié.com, @Sisi_Yemmie wacce ke bayyana ra'ayinta kan irin tsabar kudin da ake biya a makarantar ta yi mamakin dalilin da wasu ke tunanin za ta iya kai yaranta wannan makaranta.

"Charterhouse ba ta kowa ba ce," Awojide

A ra'ayin wani masani kan harkokin gudanarwa, Dr Dípò Awójídé, dama ba a samar da makarantar saboda gama-garin mutane ba.

Ya ce kaso 1% na cikin al'umma ne dama za su iya biyawa yaransu kudin makarantar.

A ganinsa, Naira miliyan 42 bai yi yawa ba, saboda Charterhouse da ke Burtaniya ana biyan £47,535 duk shekara – wanda ya haura Naira miliyan 60, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na X, @OgbeniDipo.

Ya ce makarantar dake Burtaniya ta haura shekara 400, kuma ta yaye 'ya'yan masarautar kasar da shugabanni a fannoni daban-daban.

A kalamansa:

"Na samu labarin Charterhouse na gina makaranta ta farko a nahiyar Afrika a jihar Legas a kan fili mai fadin eka 70 wanda darajarsa ta kai dala miliyan 150.”

Masanin na ganin wannan abin alfahari ne ganin yadda manyan kasar nan za su iya aika yaransu can ba tare da kashe kudin jirgi da sayen Dala ba.

An haramta wasu jami'o'in waje a Najeriya

Gwamnatin tarayya ta haramta wasu amfani da sakamakon wasu jami'o'in kasashen ketare a Najeriya biyo bayan tantamar ingancinsu.

Daga cikin manyan makarantun akwai Kwalejin Jami'ar Volta, Ho, Yankin Volta, Ghana kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

People are also reading