Home Back

Kasar Sin Na Hada Kai Da Kasa Da Kasa A Kokarin Inganta Muhallin Halittun Duniya

leadership.ng 2024/6/26
Kasar Sin Na Hada Kai Da Kasa Da Kasa A Kokarin Inganta Muhallin Halittun Duniya

Lardin Shanxi da ke arewacin kasar Sin lardi ne da aka fi yawan samun kwal a kasar Sin. Sai dai yayin da ra’ayin nan na samun bunkasuwa ba tare da gurbata muhalli ba ke kara zame wa al’ummar kasar jini da tsoka, a wannan yankin da Allah ya albarkace shi da kwal, ana ta samun sauye-sauye ta fannin nau’o’in makamashin da ake amfani da su.

Kauyen Zhuangshang wani karamin kauye ne da yawan mazaunansa bai wuce dubu ba, wanda in an duba, tamkar ba shi da bambanci da sauran kauyukan da ke arewacin kasar Sin, kawai in an lura, za a ga farantan samar da wutar lantarki ta hasken rana da aka kakkafa a rufin gidaje da ma filaye da dama na kauyen, farantan da suka samar da babban sauyi ga mazauna kauyen ta bangaren makamashi. Kowace rana da safe, da rana ta fito, to, farantan sun fara aiki ke nan, wadanda suke ta samar da wutar lantarki ga magidanta na wannan kauye, wadanda suke amfani da ita wajen dafa abinci da haskaka daki da ma sauran harkokin rayuwa, har da gudanar da ayyukan gona, matakin da ya sa mazauna kauyen suka kawo karshen yin amfani da kwal da ma sauran nau’o’in makamashi na gargajiya. Hakan kuma ya sa kauyen yin fice daga shirye-shirye sama da 2000 da aka gabatar a taron MDD kan sauyin yanayi karo na 28 da aka gudanar a bara, wanda har ya samu lambar yabo na “mai kawo sauyin fasalin makamashin da ake amfani da shi.”

Abin da ya faru a kauyen Zhuangshang wani bangare ne kawai na ci gaban da kasar Sin ta samu wajen tabbatar da bunkasuwa ba tare da gurbata muhalli ba. Alkaluman da aka samar sun shaida cewa, fadin dazuzzukan da aka dasa a kasar Sin ya kasance na farko a duniya, kuma kasar ita ce kasar da dazuzzukanta suka fi saurin karuwa a duniya, karuwar da ta kai kimanin kaso 1/4 na duk duniya cikin shekaru kusan 20 da suka wuce. Baya ga haka, a bara, karuwar yawan wutar lantarki da ake samarwa ta rana da iska da ma sauran nau’o’in makamashi masu tsabta a kasar Sin ta ninka ta kasashen kungiyar G7 har sau hudu, ta kuma ninka ta sauran kasashen duniya gaba daya fiye da sau biyu. Duk wadannan abubuwa sun faru ne sakamakon yadda tunanin nan na “kyakkyawan muhalli shi ne kadarori masu kima” ke kara zame wa Sinawa jini da tsoka a rayuwarsu ta yau da kullum. A sakamakon tunanin, duniya ta shaida yadda kasar Sin ta yi ta kara kyautata, haka kuma ta samar da gudummawa ga kyautatar muhallin halittu na duniya baki daya.

In mun dauki sabbin makamashi a misali, a cikin shekaru 10 da suka wuce, kasar Sin ta zamanto ta farko a duniya ta fannin samar da sabbin makamashi, don haka ma, ya zama wani muhimmin bangaren da kasar Sin ke aiwatar da hadin gwiwa da kasashe masu tasowa, musamman ma kasashen Afirka. A yankin De Aar da ke tsakiyar kasar Afirka ta Kudu,na’urorin samar da wutar lantarki da karfin iska, suna samar da wutar lantarki sama da KW miliyan 750 a kowace shekara, kuma ta hakan an yi tsimin kwal kimanin tan sama da dubu 200, tare da rage fitar da iskar Carbon kimanin tan dubu 700. Sai kuma a yankin Garrisa na kasar Kenya, wani kamfanin kasar Sin ya kafa tashar samar da wutar lantarki da zafin rana irinta mafi girma a gabashin Afirka, wanda ya sassauta matsalar karancin wutar lantarki da kasar ta fuskanta, kuma ba tare da fitar da iskar Carbon ba. A kasar Nijeriya, kamfanin kera bas bas na Yutong na kasar Sin, ya samar da bas bas masu aiki da wutar lantarki a birnin Lagos, karon farko ke nan da kasar ta fara samun wannan sabon nau’in motocin bas.

A kokarin da kasar Sin ke yi, an kaddamar da jerin shirye-shirye na tabbatar da ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba a dimbin kasashe masu tasowa, wadanda suka sa kaimi ga kyautatar muhallin halittun duniya.

Yau ranar kiyaye muhallin duniya ce karo na 53, haka kuma zagayowar ranar kare muhalli ta 10 ce a kasar Sin.Duniyarmu gida na bai daya ne ga dukkanin dan Adam, kuma makomar dan Adam daya ce a fannin tinkarar matsalolin muhalli. A yayin da kasar Sin ke ci gaba da kokarin inganta muhallin halittu na cikin gida, za ta kuma ci gaba da samar da gudummawa, da hada hannu da sassan kasa da kasa, musamman ma kasashen Afirka, don kara inganta muhallin duniyarmu baki daya.

People are also reading