Home Back

Faransa ta kwashe 'yan ƙasarta 170 daga Haiti saboda ta'azzarar rikici

rfi.fr 2024/4/27
Wasu 'yan sanda ɗauke da makamai a birnin Port Au Prince na Haiti mai famaa daa rikici.
Wasu 'yan sanda ɗauke da makamai a birnin Port Au Prince na Haiti mai famaa daa rikici. AP - Odelyn Joseph

Faransa ta yi amfani da wani jirgin soji mai saukar ungulu wajen kwashe ‘yan ƙasarta 170, da kuma wasu mutane 70 na’yan wasu ƙasashe daga Haiti, wadda ke fama da rikici, kamar yadda ma’aikatar harkokin wajen ƙasar ta sanar.

Sanarwar da ma’aikatar  harkokin wajen Faransa ta fitar a wannan Laraba ta ce ta kwashe ‘yan asalin ƙasarta, da ma na ’yan wasu ƙasashen da ke da rauni ne daga wannan ƙasa ta Haiti.

Ta ƙara da cewa an kai dukkannin waɗanda aka kwashe zuwa gaɓar ruwa, inda ake sa ran wani jirgin ruwan sojin ruwa zai kwashe su zuwa yankin Martinique da ke karkashin Faransa.

Ma’aikatar harkokin wajen Faransa ta ce akwai aƙalla mutane dubu 1 da dari 1 ‘yan asalin ƙasar da  ke zaune a Haiti, waɗanda da daman su  ke da damar zaman ‘yan ƙasashe  biyu.

A  ranar Lahadi ce Faransa ta sanar da aikewa da wannan jirgi, tana mai cewa duk mai sha’awar komawa gida sai ya tuntuɓi ma’aikatar harkokin wajen ƙasar a birnin Port-au-Prince.

Birnin Port-au-Prince ya sha fama da  rikicin ‘yan daba, wanda ya ɓarke a ƙarshen watan Fabrairu, lamarin da ya tilasta wa firaministan ƙasar, Ariel Henry murabus.

Sai dai duk da cewa ƙungiyoyin ’yan daban ne suka buƙaci Henry ya yi murabus, akasarin sassan babban birnin ƙasar ba su rabu da tashin hankali ba.

‘Yan ƙasar Haiti na fama da matsananciyar ƙarancin abinci a yayin da suke jiran kafuwar sabuwar gwamnatin riƙon ƙwarya.

 
People are also reading