Home Back

'Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari Masallaci, Sun Kashe Bayin Allah a Zamfara

legit.ng 2024/7/3

Jihar Zamfara - Wasu ‘yan bindiga dauke da makamai sun kai farmaki wani masallaci a ƙauyen Tazame da ke karamar hukumar Bungudu a jihar Zamfara.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Rahotanni daga yankin sun nuna cewa maharan sun kai harin ne a daidai lokacin da mutane ne shirye-shiryen Sallar Subahi ranar Talata.

Taswirar jihar Zamfara.
Yan bindiga sun harbi liman yayin da suka farmaki wani masallaci a Zamfara Asali: Original

Wani mazaunin kauyen ya shaida wa gidan talabijin na Channels cewa ‘yan bindigar sun far wa mazaunar kauyen ne a lokacin Sallar Asuba.

"Ƴan bindigar sun shiga kauyen suka kashe mutum biyu, ladanin Masallaci da kuma ƙaninsa," in ji shi.

Ya kara da cewa ƴan bindigar sun kuma harbi limamin masallacin wanda ya samu karaya a kafarsa tare da yin awon gaba da mutum kusan 10.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, ASP Yazid Abubakar, ya ceaharan sun kashe mutane biyu kun sun sace wasu da dama.

Ya ce rundunar ta tura karin jami’an ƴan sanda zuwa yankin domin dawo da zaman lafiya tare da tabbatar da ceto wadanda aka yi garkuwa da su.

"Lamarin ya faru ne da safiyar yau Talata, maharan sun kashe mutane biyu tare da yin garkuwa da wasu da dama."

"Har yanzu ba mu tabbatar da adadin mutanen da aka yi garkuwa da su ba amma rundunar ƴan sanda ta tura jami’anta yankin domin dawo da zaman lafiya.

"Haka nan kuma muna ci gaba da ƙoƙarin ceto waɗanda maharan suka sace a harin."

- ASP Yazid Abubakar.

Asali: Legit.ng

People are also reading