Home Back

Na amince zan bai wa Sanata Hanga haƙuri – Ɗahiru Mai Huddadu

dalafmkano.com 2024/6/29

Kotun majistret mai lamba 19 mai zaman ta a Nomansland a Kano, ƙarƙashin jagorancin mai Shari’a Binta Galadanci, ta sanya ranar 10 ga watan gobe dan ci gaba da sauraron ƙarar da ƴan sanda suka shigar suna ƙarar Ɗahiru Ahmad mai Huddadu bisa tuhumar ɓata suna.

Tun da fari ƴan sanda ne suka gurfanar da Mai Huddadu a gaban kotun bisa zargin bata suna.

Ƙunshin zargin ya bayyana cewar Mai Huddadun ya bata sunan sanatan Kano ta tsakiya wato Sanata Rufa’i Sani Hanga, inda ya bayyana sanatan a matsayin Ɗan sharholiya, koda yake ya musanta zargin da ake masa.

A zaman kotun na yau an zauna dan a fara sauraron shaidu, sai dai mai Huddadun ya bai wa sanatan hakuri inda shi kuma ya bayyana cewar zai haƙura amma sai mai Huddadun ya shiga kafar yaɗa labarai ya janye wancan kalaman da ya yi.

Wakilinmu na Kotu Yusuf Nadabo Isma’il ya ruwaito cewa, Mai Huddadun ya bayyana cewar zai janye kalaman nasa kamar yadda sanatan ya bukata ta kafar yaɗa labarai.

People are also reading