“Munafurci Ne”: Jarumar Fim Ta Caccaki Kiristoci Kan Murnan Auren Davido
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Lagos - Jarumar fina-finai, Merit Gold Eberechi ya jawo kace-nace a kafofoin sadarwa kan auren mawaki, Davido.
Eberechi ta ce Kiristoci sun nuna munafurci wurin taya mawakin murnan aurensa duk da haihuwar yara uku kafin aure.
Jarumar ta bayyana haka ne a shafinta na Instagram a jiya Laraba 26 ga watan Yunin 2024 inda ta nuna rashin jin dadinta kan haka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ta ce Kiristoci da dama sun taya Davido da Chioma murnan bikinsu duk da sun sani sun haifi yara uku a layin banza.
"Kiristoci suna taya Davido murnan aure duk da kowa ya sani sun haifi yara uku ba ta hanyar aure ba, amma za su caccaki mambobin cocinsu kan haka."
"A rayuwa duk yadda zaka yi kawai ka nemi kudi kafin ka yi wani kuskure da mutane za su addabe ka."
- Merti Gold Eberechi
Eberechi ta koka kan yadda ake cccakar sauran jama'a idan hakan ta faru amma idan manyan mutane ne kuma shiru za ka ji.
Ta ce ana yawan kushe mutane da ke aikata haka amma mafi yawa sai murna suke da tofa albarkacin bakinsu kan auren Davido.
Kun ji cewa Shahararren mawaki David Adeleke da aka fi sani da Davido ya gwangwaje amaryarsa, Chioma da kyautar dalleliyar mota samfurin SUV.
Motoci guda biyu da kamfanin GAC motors ya ba su a matsayin kyauta na murnar ta ya su angoncewa ya dauki hankalin masu amfani da shafukan sada zumunta.
Asali: Legit.ng