Majalisa Ta Amince a Kirkiro Hukumar Cigaban Jihohin Arewa, Za a Jira Tinubu Ya Sa Hannu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Majalisar dattawa ta yi karatu na uku a kan kudirin samar da cibiyar cigaban Arewa ta tsakiya (NCDC).
A yau Alhamis ne majalisar dattawa ta kammala karanta kudurin da aka fara shi tun cikin shekarar 2023.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa majalisar ta kammala karatun ne bayan Sanata Kaka Shehu ya gabatar da rahoto kan kudurin a gabanta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahotanni sun nuna cewa tun a ranar 5 ga watan Oktoban shekarar 2023 aka yi karatu na daya ga kudurin, rahoton Channels Television.
Sai kuma a ranar 21 ga watan Fabrairun shekarar 2024 aka masa karatu na biyu kafin a kammala karanta shi a yau.
Sanata mai wakiltar Benue ta kudu kuma shugaban marasa rinjaye a majalisa, Abba Moro ne ya gabatar da kudurin.
Daga baya kudurin ya samu goyon bayan dukkan Sanatoci masu wakiltar Arewa ta tsakiya a majalisar dattawa.
Idan shugaban kasa ya rattaba hannu kan kudurin, cibiyar za ta rika samun kudi daga gwamnatin tarayya da kungiyoyi domin yin ayyuka na musamman.
Cibiyar za ta rika ayyukan gina tituna, gidaje, makarantu, tallafawa waɗanda tsautsayi ya afka musu da sauransu.
A wani rahoton, kun ji cewa yan majalisa sun shiga fargabar yadda aka samu bazuwar gurbataccen man fetur da na dizel a kasuwannin kasar nan.
A zaman majalisar na jiya Laraba, an bayyana yadda ake zargin an kai lalataccen man da ya kai tan 660 domin sayar da su kasashen Afrika.
Asali: Legit.ng