Home Back

Majalisa Ta Amince a Kirkiro Hukumar Cigaban Jihohin Arewa, Za a Jira Tinubu Ya Sa Hannu

legit.ng 2 days ago
  • Majalissar dattawan Najeriya ta kammala karanta kudirin da zai jawo kafa cibiyar cigaba a yankin Arewa a yau Alhamis, 4 ga watan Yuli
  • Sanata mai shugabancin kwamitin ayyuka na musamman a majlisa, Kaka Shehu ne ya gabatar da rahoto kan kudirin a yau
  • Majalisar dattawa ta fara tattaunawa kan kudirin ne tun cikin shekarar 2023 da kuma farkon shekarar 2024 kafin kammala karatun a yau

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Majalisar dattawa ta yi karatu na uku a kan kudirin samar da cibiyar cigaban Arewa ta tsakiya (NCDC).

A yau Alhamis ne majalisar dattawa ta kammala karanta kudurin da aka fara shi tun cikin shekarar 2023.

Majalisa
Za a kafa cibiyar cigaba a Arewa ta tsakiya. Hoto: Nigerian Senate Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa majalisar ta kammala karatun ne bayan Sanata Kaka Shehu ya gabatar da rahoto kan kudurin a gabanta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yaushe aka gabatar da kudurin?

Rahotanni sun nuna cewa tun a ranar 5 ga watan Oktoban shekarar 2023 aka yi karatu na daya ga kudurin, rahoton Channels Television.

Sai kuma a ranar 21 ga watan Fabrairun shekarar 2024 aka masa karatu na biyu kafin a kammala karanta shi a yau.

Wani Sanata ya gabatar da kudurin a majalisa?

Sanata mai wakiltar Benue ta kudu kuma shugaban marasa rinjaye a majalisa, Abba Moro ne ya gabatar da kudurin.

Daga baya kudurin ya samu goyon bayan dukkan Sanatoci masu wakiltar Arewa ta tsakiya a majalisar dattawa.

Wane aiki cibiyar za ta yi?

Idan shugaban kasa ya rattaba hannu kan kudurin, cibiyar za ta rika samun kudi daga gwamnatin tarayya da kungiyoyi domin yin ayyuka na musamman.

Cibiyar za ta rika ayyukan gina tituna, gidaje, makarantu, tallafawa waɗanda tsautsayi ya afka musu da sauransu.

Majalisa ta koka kan gurbataccen mai

A wani rahoton, kun ji cewa yan majalisa sun shiga fargabar yadda aka samu bazuwar gurbataccen man fetur da na dizel a kasuwannin kasar nan.

A zaman majalisar na jiya Laraba, an bayyana yadda ake zargin an kai lalataccen man da ya kai tan 660 domin sayar da su kasashen Afrika.

Asali: Legit.ng

People are also reading