Home Back

Ƴan Majalisa na so a gaggauta siya wa Tinubu da Shettima sabbin jirage na zamani

premiumtimesng.com 2024/7/3
Tinubu ya tafi hutu Landan da Paris, daga can zai zarce Umrah

Kwamitin Majalisar Tarayya masu Lura da Fannin Tsaro da Leƙen Asiri, sun yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta gaggauta sayen sabbin jirage gadagau ga Shugaban Ƙasa Bola Tinubu da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima.

Wannan kira ya zo ne daidai lokacin da ake ta ƙadabolo tsakanin ƙungiyoyin ƙwadago na NLC, TUC da kuma Gwamnatin Tarayya.

Kwamitin ya yi wannan kira a cikin wani rahoto da ya miƙa, bayan wani ƙaramin kwamiti ya gudanar da zaman sauraren irin halin inganci da nagartar da jiragen shugaban ƙasa ke ciki.

“Kwamitin ya gamsu cewa akwai buƙatar gaggawa domin a sayo wa Shugaban Ƙasa da Mataimakin Shugaban Ƙasa sabbin jirage. Hakan zai kawai da fargaba ko shakkun afkuwar wani abin da ba fatan afkuwar sa ake ba.”

PREMIUM TIMES ta samu rahoton wanda Shugaban Kwamiti, Ahmed Satomi da Magatakardar Majalisa, Makwe Eric suka sa wa hannu.

Wasu ‘yan majalisar sun ce tuni har ma an aika wa Shugaban ƙasa rahoton, domin ya ɗauki matakin da ya dace.

Rahoton dai ya ce akwai jirage shida a bargar jiragen Shugaban Ƙasa. Sai kuma helikwafta guda shida, waɗanda biyu daga cikin su ko an yi masu garambawul ba za su iya cirawa sama ba.

Kwamitin ya ce jirgin da shugaban ƙasa ke hawa ya kai shekaru 19, kuma samfurin Boeing 737 ne, kuma a yanzu haka ya na can ana yi masa garambawul na shekara-shekara.

Shi kuwa na Mataimakin Shugaban Ƙasa, shekarar da 13, kuma samfurin Gulfstream G550 ne, amma lafiyar sa ƙalau.

People are also reading