Home Back

Bayan APC Ta Buƙaci Cafke Shi, Kwankwaso Ya Tura Sako Ga Tsohon Gwamna

legit.ng 2024/7/3
  • Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya jajantawa tsohon shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki kan rasuwar mahaifiyarsa
  • Kwankwaso ya tura sakon ta'aziyya bayan rasuwar Florence Morenike Saraki a jiya Talata 18 ga watan Yuni
  • Tsohon gwamnan jihar Kano ya yi addu'ar samun rahama ga marigayiyar tare da ba iyalanta hakurin wannan babban rashi da suka yi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Jigon siyasar jihar Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso ya tura sakon ta'aziyya ga Bukola Saraki.

Kwankwaso ya jajantawa Saraki kan rasuwar mahaifarsa a jiya Talata 18 ga watan Yuni da muke ciki.

Sanatan ya bayyana haka a yau Laraba 19 ga watan Yuni a shafinsa na X inda ya jajantawa iyalan marigayiyar.

Marigayiya Florence Morenike Saraki ta rasu ne bayan fama da jinya kamar yadda tsohon shugaban Majalisar ya tabbatar.

Tsohon gwamnan Kano daga bisani ya yi addu'ar samun rahama a gare ta da yafiya daga Ubangiji madaukakin Sarki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma roki Allah ya ba iyalan marigayiyar hakurin jure wannan babban rashi da suka yi na uwa.

"Ina mika sakon ta'aziyya ga mai girma Bukola Saraki da iyalansa da kuma al'ummar jihar Kwara kan rasuwar Florence Morenike Saraki."
"Ina addu'ar ubangiji ya mata rahama ya kuma ba iyalanta hakurin jure wannan rashin da suka yi."

- Rabi'u Musa Kwankwaso

Mahaifiyar Bukola Saraki ya rasu

A wani labarin, kun ji cewa tsohon shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki ya sanar da rasuwar mahaifiyarsa.

Tsohon gwamnan Kwara, Saraki ya sanar da rasuwar Florence Morenike Saraki a jiya Talata 18 ga watan Yuni a shafinsa na X.

Asali: Legit.ng

People are also reading