Home Back

Gwamnan Kano ya kafa kwamiti guda biyu da zai binciki tsohuwar gwamnatin Ganduje

dalafmkano.com 2024/5/18

Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da wani kwamati guda biyu da za su bincike akan yadda tsohuwar gwamnatin Dr Abdullahi Umar Ganduje ta gudanar da tafiyar da gwamnatin ta a shekaru takwas da suka gabata.

Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ne ya jagoranci ƙaddamar da kwamititocin, wanda kwamitin na farko zai yi bincike akan yadda akayi tasarrafi da kadarorin gwamnati na ciki da wajen jihar kano, wanda suke zargin an sayar ko mallakawa kai da kuma mallaka wa ‘ya’ya ba bisa ka’ida ba.

Kwamati na biyu kuma da zai yi bincike akan yadda aka gudanar da rikice rikicen zabe, da yadda akayi amfani da matasa wajen tayar da hankali da salwantar da rayukan al’ummar da ba suji ba kuma basu gani ba.

A cewar gwamnan, “A bisa zargin da muke yiwa tsohuwar gwamnatin ta Ganduje, ne ya sa muka naɗa ingantattun mutane, da za su kwashe tsawon watanni uku suna gudanar da wannan bincike, “in ji Gwamna Abba Kabir”.

Ya kuma ƙara da cewa wannan bincike ba sunayin sa ba ne domin muzgunawa wani ko wata, ya ce alkawarin da suka yiwa al’ummar jihar kano, da kuma rantsuwa da su kayi da Al-kur’ani, ne ya sa zasu gudanar da wannan bincike.

Abba Kabir, yana mai cewa duk wanda aka kama da laifi za’a hukunta shi kamar yadda doka ta tanadar.

Wakilinmu na fadar gidan gwamnatin Kano Abba Haruna Idris, ya rawaito wamnan ya kuma ja hankalin kwamitin da suyi bincike mai karfi a bangaren yadda aka gudanar da yanke – yanken gonaki da burtalai, da makarantu da makabartu domin mayarwa da al’ummar jihar kano hakkinsu, ya kuma ja hankalin Kwamatin da suyi aiki tsakani da Allah yayin gudanar da binciken.

People are also reading