Home Back

Na’urorin Kula Da Iyakokin Kasa Za Su Fara Aiki Ba Da Jimawa Ba – Ministan Cikin Gida

leadership.ng 2024/7/6
iyakokin kasa

Gwamnatin tarayya ta ce dukkanin iyakokin kasar nan an jibge musu na’urorin sanya ido masu sarrafa kansu domin inganta tsaron kasar da za su fara aiki nan ba da jimawa ba.

Ministan kula da harkokin cikin gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, shi ne ya shaida hakan a cikin makon nan a lokacin duba aikin da ake yi na ginawa da zuba kayan aiki a cibiyar kula da ba da umarni na mashiga ta fasahar zamani a filayen jiragen sama da kuma cibiyoyin tattara bayanai na kan iyakoki wadanda suke cikin shalkwatar hukumar kula da shige da fice ta kasa (NIS).

Ya nuna gamsuwarsa da yadda ake gudanar da aiki mai inganci kuma cikin hanzari, ya lura kan cewa aikin farko na sanya na’uorin sa ido a iyakoki za su kammalu a watan Oktoban 2024.

Ya sanar da cewa ginawa da sanya kayan aiki a cibiyar ba da umarnin da kula da ke NIS ya kammalu kaso dari bisa dari, wanda ana jiran kaddamar daga Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu zai jagoranta. Ya kuma ce aikin sa ido kan iyakoki na zamani ya kai kaso 60 cikin dari na kammaluwa.

“Muna zaman jiran shugaban kasa ne domin kaddamarwa. TunI muka sanar da shugaban kasa kuma ina farin cikin sanar da ‘yan jarida cewa aikin an kammala shi 100 bisa 100.”

Tunji-Ojo ya kara da cewa tsarin sa ido kan iyakoki mai amfani da kansa na zamani zai taimaka wajen dakile aikata laifuka a iyakoki da kuma samun damar bibiyar iyakoki tun daga shalkwatar NIS kai tsaye.

Ministan ya jaddada cewa kula da tsaron iyakoki na da muhimmanci kuma na daga cikin muhimman abubuwan da Shugaban Tinubu ba zai yi sako-sako da su ba domin tabbatar da tsaro da kare ‘yan kasa.

Kwanturola janar na hukumar shige da fice, Kemi Nanna Nandap, ta bayyana cewa an horas da jami’ansu yadda za su tafiyar da sabbin na’urorin da ke aiki da kansa, inda ta ce a yanzu haka ma wasu jami’an na samun horo kan hakan.

Nandap ta kara da cewa al’ummomin da suke iyakokin kasar su ma an wayar musu da kai kan irin gudunmawar da ake fatan za su bayar domin cimma nasarorin da aka sanya a gaba ciki har da bayar da muhimman bayanan da suka dace ga NIS a duk lokacin da bukatar hakan.

People are also reading