Ana binciken jirgin mataimakin shugaban Malawi da ya bace
Ana ci gaba da bincike domin gano jirgin saman da ke ɗauke da mataimakin shugaban ƙasar Malawi, Saulos Chilima.
Jirgin saman ya ɓace ne a ranar Litinin da safe.
Ana tunanin ya faɗi ne a dajin Chikangawa Forest da ke arewacin ƙasar.
Ya fuskanci rashin kyawun yanayi abin da ya sa aka hana jirgin sauka a filin jirgin sama na Mzuzu.
Shugaban Malawi ya ce ya ba da umarnin a ci gaba da aikin ceto mataimakinsa Saulos Chilima har sai an gano jirgin da ke ɗauke da shi da wasu mutane tara.
Shugaba Lazarus Chakwera ya ce babu shamaki da za a sanya wa aikin.
Ya ce yana cike da fatan gano mutanen da ransu.
Ana sa ran mataimakin shugaban kasar da ya ɓace zai yi takara da mai gidansa shugaba Chakwera a zaɓen shugaban ƙasar na shekara mai zuwa.
Kafin shiga harkokin siyasa, Dr Chilima ya riƙe muƙamai a manyan kamfanoni kamar Unilever da kuma Coca Cola.
Shekarunsa 51. Yana da mata da ƴa ƴa biyu.
Shafin gwamnati ya bayyana Dr Chilima a matsayin "mai aiki tuƙuru" wanda "ba ya gajiya".