Home Back

A karo Na 7, Sayyada Sadiya Haruna, Tsohuwar Matar G Fresh Zata Amarce

legit.ng 3 days ago
  • A yau Juma'a ne za a daura auren fitacciyar jarumar TikTok, Sayyada Sadiya Haruna, tsohuwar matar G-Fresh Al'amin
  • Ita da kanta Sadiya Haruna ta wallafa katin daurin auren mai dauke da sunan angon da za ta aura, Hon. Babagana Audu Grema
  • Wannan ne karo na bakwai da za ta yi aure kamar yadda ta sanar a zauren hirar da tayi da Hadiza Gabon, fitacciyar jarumar Kannywood

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Borno - A yau Juma'a, 5 ga Yulin 2024, fitacciyar jarumar TikTok kuma mai siyar da kayan mata, Sayyada Sadiya Haruna za ta yi aure karo na bakwai.

Sadiya Haruna ta dora katin gayyatar zuwa daurin aurenta, wanda za a yi a Maiduguri dake jihar Borno.

Sayyada Sadiya Haruna za ta amarce a karo na 7
Sayyada Sadiya Haruna, tsohuwar matar G-Fresh za ta sake yin wani auren karo na 7. Hoto: Sayyada Sadiya Haruna Asali: Facebook

Aminiya ta rahoto cewa, sunan sabon angon Honarabul Babagana Audu Grema kuma yana zuwa jim kadan bayan kashe aurenta da shahararren dan TikTok, G-Fresh Al-Amin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rabuwar aurenta da G-Fresh

Auren mawakiyar begen Annabin bai yi tsawon kwana da jarumin TikTok din ba.

A halin yanzu takaddama kala-kala ce ta dabaibaye dalilin rabuwar su tun bayan da kotun addinin Musulunci ta shiga tsakaninsu.

Sayyada Sadiya Haruna ta sanar da cewa, ta biya shi kudi har N500,000 domin ta fanshi kanta daga igiyoyin aurensa.

Rikicin Sadiya Haruna da G-Fresh dai ya bazu a kafofin sada zumunta inda ake ta tofa albarkacin baki musamman bayan hirarsu da Hadiza Gabon.

Hadiza Gabon ta tattauna da sayyada

A yau mako daya kenan da Hadiza Gabon ta saki tattaunawa da Sayyada Sadiya inda ta bayyana dalilin rabuwarta da tsohon mijinta.

A nan ne ta bayyana irin dambarwar da ta shiga tsakaninsu har lamarin da ya kai ga rabuwarsu.

Ta fara da bayyana cewa, a farko yaronta ne kuma ko a mafarki bata taba tsammanin za ta taba aurensa ba.

Amma kaddara wacce ta riga fata ta hada su kuma haka suka yi aure wanda bai ko dade ba.

Auren Sadiya Haruna da G-Fresh ya mutu

A wani labari na daban, jita-jitar mutuwar auren Sayyada Sadiya Haruna ta fara ne tun watan Yulin shekarar 2023. Wata daya tak bayan da aka daura mata aurenta da G-Fresh Al'amin.

An fara batun mutuwar auren ne bayan da Sadiya ta cire dukkanin hotuna da bidiyoyinsu tare a kafar sada zumunta, wanda ya kyasta wutar jita-jitar.

Asali: Legit.ng

People are also reading