Home Back

NLC: Bola Tinubu Ya Samu Saƙon Mafita Kan Mafi Ƙarancin Albashi a Najeriya

legit.ng 2 days ago
  • Yayin da tattaunawa ta tsaya cak kan mafi ƙarancin albashi, wani jagoran ƴan kwaɗago, Akeem Ambali ya tura saƙo ga Bola Ahmed Tinubu
  • Ambali ya roƙi kwamitin sabon mafi ƙarancin albashi da Shugaba Tinubu su zama masu riko da gaskiya a tattaunawar da ake yi
  • Ƴan kwadago dai sun gabatar da N250,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi, adadin da ya gwamnatin tarayya ta ce ya wuce ƙima

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Akeem Ambali, ma'ajiyin ƙungiyar kwadago ta ƙasa (NLC) ya roƙi Bola Ahmed Tinubu ya miƙa kudirin sabon mafi karancin albashi ga majalisa.

Ambali ya bayyana cewa bai kamata Tinubu ya tsaya wani jinkiri ba bayan ya tuntuɓi ƴan kwadago kuma sun samu matsaya.

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Wani kusa a NLC ya bai wa Bola Tinubu shawara kan sabon mafi ƙarancin albashi Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Asali: Facebook

Ya bai wa Tinubu wannan shawara ne a lokacin da yake jawabi yayin hira da jaridar Punch ranar Asabar, 29 ga watan Yuni, 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jami'in na NLC ya shawarci Shugaba Tinubu da "ya mayar da hankalinsa wajen tattaunawa da ƴan kwadago tare da da alƙaluman halin da ake ciki na gaskiya."

Ambali ya jaddada buƙatar samar da albashin da ya dace, inda ya roki masu ruwa da tsaki su zama masu gaskiya a sabuwar tattaunawar da za a ɗora nan gaba.

"Kwamiti ne mai ɓangarori uku, biyu sun haɗu a wuri ɗaya saboda suke da ma'aikata, sai kuma ragowar bangare ɗaya wanda biyu ne suka zama ɗaya watau ma'aikata.
"Ma'aikata ne kaɗai suke ta tayar da jijiyoyin wuya saboda su suka san wahalar da suke sha, komai kansu yake ƙarewa. Ya kamata shugaban kasa ya mayar da hankali wajen zama da ƴan kwadago.
"A zo da alkalin kididdiga na gaskiya nawa ke iya riƙe iyali a wata? Wannan ya zame mana jagora, idan muka amince da haka, to komai zai zo da sauƙi."

- Akeem Ambali.

Gwamnan Jigawa ya faɗi shirinsa

A wani labarin kun ji cewa Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa ya ce har yanzu gwamnatin jihar ba ta yanke adadin da zata biya a mataayin sabon mafi karancin albashi ba.

Namadi ya bayyana cewa gwamnatin Jigawa ba ta ma fara tattaunawa kan ƙarin albashi da ƙungiyar kwadago ta jihar ba.

Asali: Legit.ng

People are also reading