Home Back

Tinubu Ya Kirkiro Sababbin Jami’an Tsaro a Najeriya, an Bayyana Aikin da Za Su Rika Yi

legit.ng 2024/7/6
  • Gwamnatin Najeriya ta kirkiro sababbin jami'ai domin magance matsalolin tsaro a manyan filayen jiragen sama da ke Najeriya
  • An kaddamar da sababbin jami'an tsaron ne a babban filin jirgin saman Janar Murtala Muhammad a birnin Legas a makon nan
  • Gwamnatin Najeriya ta bayyana yadda jami'an tsaron za su cigaba da aiki da kuma yadda za fadada ayyukansu zuwa wasu jihohi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Lagos- Gwamnatin Najeriya karkashin Bola Tinubu ta kirkiro jami'an tsaron filayen jiragen sama (AVSEC).

Rahotanni sun nuna cewa an kaddamar da jami'an tsaron ne a jiya Litinin a filin jirgin saman Murtala Muhammad da ke Legas.

Jami'an AVSEC
An kirkiro jami'an tsaron filayen jiragen sama a Najeriya. Hoto: FAAN Asali: Facebook

Ministan harkokin filin jiragen saman, Festus Keyamo ya bayyana irin ayyukan da jami'an tsaron za su rika yi a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin ƙirƙiro jami'an tsaron filin jirgi

Ministan harkokin filin jiragen sama, Festus Keyamo ya bayyana cewa an kirkiro jami'an taron ne domin bayar da cikakkiyar kariya a filayen jiragen sama.

Festus Keyamo ya tabbatar da cewa dama sun yi alkawarin tsaftace filayen jiragen saman Najeriya kuma sun cika alkawarin.

Ayyukan da jami'an AVSEC za su yi

Festus Keyamo ya bayyana cewa jami'an za su rika kama duk wanda ya yi kokarin yin wata barna ko tayar da hankali a filayen jiragen sama.

Keyamo ya kara da cewa wannan matakin sharar fage ne wajen tabbatar da sun hana jami'an gwamnati rokon matafiya kudi da cutarsu.

Gwamnati za ta fadada jami'an AVSEC

Har ila yau, ministan ya bayyana cewa da sannu za a fadada jami'an AVSEC zuwa sauran filayen jiragen saman kasa da kasa da ke Najeriya.

Hukumar FAAN ta wallafa a shafinta na Facebook cewa sababbin jami'an za su samar da aminci ga matafiya a filayen jiragen sama.

Tinubu zai karbi filayen jiragen sama

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya rubuta wasika ga majalisar dattawa domin neman izinin biyan jihohin Nasarawa da Kebbi N24.6bn.

Shugaban Bola Tinubu ya bayyana cewa za a biya jihohin kudaden ne bayan gwamnatin tarayya ta karbi filayen jiragen saman su.

Asali: Legit.ng

People are also reading