Home Back

Isra'ila da Hezbollah na yi wa juna barazana da wuta amma ba sa son yaƙi tsakaninsu

bbc.com 2024/7/6

Asalin hoton, Getty Images

Isra'ila ta yi ta faman kashe gobara a arewacin ƙasar waɗanda hare-haren Hezbollah suka haddasa a 'yan makonnin nan
Bayanan hoto, Isra'ila ta yi ta faman kashe gobara a arewacin ƙasar waɗanda hare-haren Hezbollah suka haddasa a 'yan makonnin nan
  • Marubuci, Lucy Williamson
  • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakiliyar Gabas ta Tsakiya

An samu wani juyi na siyasa sakamakon rikici tsakanin Isra'ila da ƙungiyar Hezbollah ta Lebanon ya kai wani mataki a makon nan.

Musayar wutar da aka saba gani ta sauya saboda bikin Idin Babbar Sallah, inda aka maye gurbinsu da barazana kamar wadda aka sani idan ana shirin fara yaƙi.

Shugaban Hezbollah Hassan Nasrallah ya yi barazanar a ranar Laraba ta kutsawa arewacin Isra'ila idan har yaƙi ya ɓarke tsakaninsu da ƙasar.

Ya kuma ce Hezbollah na da "sababbin makamai" da za a gani a fagen dagar.

Amma ya ƙara da cewa ƙungiyar ba ta son yaƙi gaba da gaba da Isra'ila - kuma tana kallon hare-haren da take kaiwa a matsayin tallafi ga 'yan gwagwarmayar Falasɗinawa a Zirin Gaza.

A ranar Laraba Hizbollah ta saki wani hoton bidiyo da aka ɗauka daga jirgi maras matuƙi na birnin Haifa, inda aka nuna wurare masu muhimmanci na gine-ginen farar hula da kuma na soji. Ana kallon hakan a matsayin wata babbar barazana ga Isra'ila don kada ta zafafa - kai hari mummuna a Haifa kai iya haifar da cikakken yaƙi tsakaninsu.

Nasrallah ya ce hakan wani salon yaƙin Hezbollah ne "na rikita abokin gaba" kan maƙiya.

'Yan awanni bayan sakin bidiyon, Ministan Harkokin Wajen Isra'ila Israel Katz ya ce "ƙasar ta kusa cimma matsaya wajen sauya matakin da za ta ɗauka kan Hezbollah da Lebanon".

Idan aka fara yaƙi gadangadan, in ji shi, "za su tarwatsa Hezbollah kuma Lebanon za ta ji jiki".

Rundunar sojin Isra'ila ta ce "an amince da wani shiri na kai hari cikin Lebanon".

Ana ganin dukkansu ba su son yaƙi a yanzu. Irin wannan yaƙi - tsakanin abokan gaba masu ƙarfi - zai shafi miliyoyin farar hula a ɓangarorin biyu, kuma zai iya jawo uwar gidan Hezbollah wato Iran da kuma uwar gidan Isra'ila wato Amurka su shiga rikicin.

Amma kuma abu ne mai wuya a iya tantance gargaɗi da kuma yunƙurin fara yaƙi tsakanin ɓangarorin.

Asalin hoton, Getty Images

An Israeli firefighter and a resident take cover as sirens sound to warn of rockets launched from southern Lebanon, in Kiryat Shmona in northern Israel near the Lebanese border on June 19, 2024.
Bayanan hoto, Israelis duck for cover as sirens warn of rockets launched over the border from southern Lebanon

Wasu daga cikin muƙarraban gwamnatin Isra'ila na ganin harin da Hamas ta kai cikin ƙasar ranar 7 ga watan Oktoba sun sauya tunani game da tsaron ƙasar, kuma mazauna arewacin ƙasar ba za su iya komawa gidajensu ba har sai an kawo ƙarshen Hezbollah.

Mazauna arewacin da yawa sun yarda da hakan.

Sama da 60,000 daga cikinsu na zaune a matsugunai da ke nesa da iyakar Lebanon da Isra'ilar tun daga lokacin da Hezbollah ta fara kai hare-haren roka da makamai masu linzami don nuna goyon baya ga ƙungiyar Hamas ƙawarta.

Haka ma 'yan Lebanon sama da 90,000 sun bar gidajensu saboda martanin da sojojin Isra'ila ke mayarwa ta sama.

Ra'ayin wasu 'yan Isra'ila 800 a makon nan da cibiyar People Policy Institute ya gano cewa kashi 60 cikin 100 na son a kai wa Hezbollah hari "da ƙarfin tsiya".

Sama da kashi ɗaya cikin uku (kashi 36 cikin 100) na son a kai hare-haren "cikin gaggawa" - tun kafin ma Isra'ila ta gama yaƙi da Hamas a Gaza. Yawan masu wannan ra'ayin ya ƙaru bayan gudanar da irin wannnan ƙuri'ar wata uku da suka wuce.

Yaƙin Gaza na cikin dalilan da suka sa Isra'ila ka iya yin ɗari-ɗari kafin ta ƙaddamar da wani yaƙin da Hezbollah, wana ya fi na Gaza wahala sosai, a lokaci guda.

A wannan wata Isra'ila ta ƙara yawan dakarun ko-ta-kwana da za a iya kirawowaa kowa ne lokaci zuwa filin yaƙi, daga 300,000 zuwa 350,000, abin da ya sa ake ganin akwai yiwuwar fafata yaƙi a arewacin.

Haka nan, kowane ɓangare na cigaba da faɗaɗa wuraren da yake kai wa hari tsawon wata takwas yayin da hare-haren ke ƙara tsanani.

'Yan kwanaki kafin Idin Babbar Sallah, an ga yadda makaman roka daga Lebanon suka dinga sauka a Isra'ila bayan kashe kwamandan Hezbollah Taleb Abdallah.

Hare-haren ramuwar tsakaninsu kan kai ga cikakken yaƙi idan wani ya kai mummunan hari kan wani babban wuri, ko kuma ya kashe mutane da yawa.

Zuwa yanzu Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ta ce mutum 400 aka kashe a Lebanon, cikinsu har da farare hula masu yawa.

Aƙalla mutum 25 - sojoji da fararen hula - aka kashe a Isra'ila.

Asalin hoton, Getty Images

Hezbollah ta harba ɗaruruwan makamai zuwa arewacin Isra'ila bayan kashe mata babban kwamanda Taleb Abdallah ranar 11 ga watan Yuni
Bayanan hoto, Hezbollah ta harba ɗaruruwan makamai zuwa arewacin Isra'ila bayan kashe mata babban kwamanda Taleb Abdallah ranar 11 ga watan Yuni

Amurka ta tura wakilinta na musamman zuwa duka ɓangarorin a wannan makon domin shawo kan matsalar, amma Hezbollah ta fayyace ƙarara cewa tana taya Hamas ƙwarta yaƙi ne, kuma tsagaita wuta a Gaza ana ganin shi kaɗai ne zai dakatar da rikici a arewacin.

Amma a wajen Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, wanda ke shan matsin lamba don kawo ƙarshen yaƙi, cigaba da yaƙin zai amfane shi.

Abu ne mai wuya ya iya cewa ya yi nasara a Gaza ba tare da kashewa ko kama shugabannin Hamas ba, yayin da kuma har yanzu ƙungiyar na da bataliyoyi a zirin.

Da ma can neman ƙarin lokaci ɗaya ne daga cikin abubuwan da Netanyahu ya fi ƙwarewa a kai.

Yanzu dai ɓangarorin biyu na wasa da wuta.

People are also reading