Home Back

Mahaifi Ya Lakaɗawa Malamar Makarantar Abuja Duka Saboda Ta Taba Yarinyarsa

legit.ng 2024/7/1
  • An samu rigima a wata makaranta a birnin tarayya Abuja bayan wani mahaifi ya je har makarantar ya da daki malama
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa malamar tana rike da 'yar ta mai wata uku a duniya mutumin ya afka mata da duka
  • Mahaifin mai suna Muhammad Jimeta ya bayyana dalilan da suka sa shi dukan malamar duk da cewa tana shayarwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - An samu rigima a makarantar Aces da ke birnin tarayya Abuja bayan wani mahaifi ya shiga harabar makarantar ya lakaɗawa malama duka.

Rahotanni sun nuna cewa mahaifin mai suna, Muhammad Jimeta yana da 'diya 'yar aji uku a makarantar.

Malami
Mahaifi ya daki malamar makaranta a Abuja. Hoto: James Marshall Asali: Getty Images

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Muhammad Jimeta ya jibgi malamar makarantar mai suna Sekinat Adedeji ne a lokacin da ta ke rike da jariri ɗan wata uku da haihuwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayani daga bakin malama Sekinat Adedeji

Malamar ta labarta cewa lamarin ya fara ne a lokacin da ta umurci dalibai masu surutu su kafa gwiwa a kasa.

Sai 'yar mutumin mai suna Karima Muhammad Jimeta ta yi rashin kunya wajen zagin malamar saboda haka sai malamar ta kwada mata lura a kafa.

Mahaifi ya bugi malamar 'yarsa a Abuja

Bayan an tashi daga makaranta sai mahaifin Karima ya zo zai dauke su da misalin karfe 4:00 na yamma.

Da zuwan mahaifin sai Karima ta fada masa abin da ya faru shi kuma sai ya fara marin malamar sai da ya mata har mari hudu.

Mahaifi: "Dalilin dukar malamar 'diyata"

Malam Muhammad Jimeta ya bayyana cewa malamar ta saba dukan 'yar sa a makarantar tun kafin ranar, rahoton the Guardian.

Ya kuma tabbatar da cewa ya kai korafi ga hukumar makarantar amma aka ba shi hakuri a lokacin.

Amma duk da haka malamar ta nuna masa gadara cewa ba za ta daina dukan 'yar sa ba, saboda haka ne ya dauki matakin.

An harbi malamar makaranta a Amurka

A wani rahoton, kun ji cewa wani dalibi dan shekara shida a wata makarantar firamare a jihar Virginia a kasar Amurka ya bindige malamar makaranta.

Steve Drew, shugaban yan sanda na yankin ya tabbatar da afkuwar lamarin, yana mai cewa malamar tana asibiti rai a hannun Allah.

Asali: Legit.ng

People are also reading