Home Back

Saboda tsananin bashin da gwamnatin baya ta tattago, ko albashi wuyan biya yake mana a Kaduna – Uba Sani

premiumtimesng.com 2024/5/3
Ba mu ɗauko hayar mai shiga tsakani domin karɓo ɗaliban Kuriga daga hannun Ƴanta’adda ba – Gwamnatin Kaduna

Gwamna Uba Sani na Kaduna ya bayyana cewa matsalolin da jihar ke fuskanta a yanzu sun haɗa da ƙarancin kuɗi d jihar ke dama da shi.

Uba ya bayyana wa dandazon ƴan Kaduna a wurin taron cewa kudin da jihar ke amsa daga gwamnatin tarayya ba ya isa koda albashi ne jihar ta biya.

” A watan Maris, mun karbi naira biliyan 10 daga gwamnatin tarayya, amma kuma bayan bankuna sun zaftare basukan su, mun tsira ne da naira biliyan 3 kacal a watan da ko albashin ma’aikatan mu ba za mu iya biya ba.

Gwamna Sani ya ce naira biliyan 5.5 ne ake biyan albashin ma’aikatan Kaduna, amma naira biliyan 3 kacal gwamnati ke tsira da shi byan bankuna sun zaftare basukan da gwamnatin baya ta ci.

” Abin farinciki gare ni shine zan sanar muku duk da ɗinbin wannan bashi da muka gada, ba mu ciwo bashin kowa ba.

A wata sabuwar faifan siyasa da a ka buɗe a jihar Kaduna, a yau Asabar, gwamnan jihar Uba Sani, ya tabbatar da hannun riga da ya yi da tsohon gwamnan Jihar, Nasir El-Rufai inda ya bayyana cewa tsohon gwamnan ya karankatako ɗinɓin basuka daga kasashen waje a lokacin da ya ke gwamnan jihar.

Gwamna El-Rufai ne gwamnan Kaduna daga 2015-2023, inda bayan ya kammala wa’adin sa ya ɗora Uba Sani a matsayin gwamnan jihar.

Sai dai kuma da yawa daga cikin masu yi wa siyasar Kaduna fashin baki ba su ɗauka hakan zai faru tsakanin gwanayen biyu ba da wuri haka.

Gwamna Sani a wurin wani taro a Kaduna ranar Asabar ya bayyana cewa hatta albashi na yi masa wuyan biya ne saboda ɗinbin bashin da El-Rufai ya tattago a lokacin da yake gwamnan jihar.

Gwamna Sani na jihar Kaduna ya bayyana cewa ya gaji bashin da ya kai $587m, N85bn da kuma bashin kwangiloli 115 daga gwamnatin da ta shude ta Nasir El-Rufai, inda ya koka da yadda a dalilin bashin ko an turo wa jihar kudi daga asusun tarayya ba ta samun wani abin kirki.

Sai dai kuma bayan kammala wannan taro, ɗan El-Rufai, Bashir El-Rufai a shafinsa ta X ya maida wa gwamnan da martani inda ya ce ” Maimakon Uba sani ya kawai fito fili ya nuna ya gaza, ya boye bayan wai bashin da aka ciwo ne wai yake haba shi aiki a jihar.

” Kawai waɗannan mutanen sun gane ba za su iya wa mutane komai ba ne sai suke karkata zuwa wani abun.

” Daga gwamnan su wanda ya maida ofishin sa Abuja, sai tarin ƴan yuyuyu da ya naɗa wai mataimakan sa, kawai don ya saka musu a siyasance, maimakon naɗa fitattu, kwararru, gogaggu, ya fake da an ciwo bashi ba ya komai.

People are also reading