Home Back

Ana bikin ranar Dimukradiyya a Najeriya

bbc.com 2024/10/7
.

Asalin hoton, Bola Ahmed Tinubu

Larabar nan, 12 ga watan Yuni ce ranar da yan Najeriya ke murnar zagayowar ranar Dimokuradiyya a kasar, da aka fi sani da June 12.

Wannan rana ce da tarihin kasar ba zai manta da ita ba saboda a ranar ne aka gudanar da zaben Najeriya na 1993, wanda ake kallo a matsayin mafi tsarki, ko da yake a zahiri ya bar baya da ƙura.

Tsohuwar gwamnatin ƙasar ta shugaba Muhammadu Buhari ce ta sauya ranar, daga 29 ga watan Mayu, ranar da aka fara gudanar da mulkin farar hula zuwa 12 ga watan Yuni, ranar da aka gudanar da zaben na 1993.

Albarkacin wannan rana gwamnati ta ayyana Larabar nan a matsayin ranar hutu, don gudanar da bukukuwa, kana shugaba Bola Ahmed Tinubu zai gabatar wa yan kasar jawabi na musamman.

Ana kyautata zaton cewar ɗan takarar jam'iyyar SDP, wato Moshood Olawale Abiola ne ya lashe zaɓen bayan da ya kayar da abokin takararsa na jam'iyyar NRC Bashir Othman Tofa.

An dai ki sanar da sakamakon zaben ne saboda soke zaben da gwamnatin mulkin soja a karkashin mulkin Janar Ibrahim Badamasi Babangida ta yi.

Sai dai a bana ranar ta zagayo a lokacin da yan kasar da dama ke fama da matsaloli iri-iri, musamman na tsaro da tashin farashin kayan masarufi.

'Yan Najeriya na mantawa da wannan rana'

Mannir Dan-Ali, tsohon ma’aikacin BBC, kuma mai sharhi kan lamuran yau da kullum a Najeriyar, ya ce akwai takadama a kan wannan rana, inda wasu da dama ke mata kallon wani kokari da jama'ar yankin Yarbawa ke yi na fifita al'amuransu da kuma gwagwarmayar da suka yi.

''Masu rajin wannan rana bayan da suka kafa gwamnati tare da Buhari ne suka yi kokarin sauya ta zuwa ranar 12 ga watan Yuni, amma kwai mutane da dama da ke ganin cewa ranar da aka fara mulkin dimukradiyya karkashin farar hula, wato 29 ga watan Mayu ce ta fi dacewa a matsayin ranar Dimukradiyya'' in ji shi.

Ranar Dimukradiyya ta kara karfi ne zamanin tsohon shugaban ƙasar Muhamadu Buhari, wanda ya sauya ta zuwa 12 ga watan na Yuni.

An soma gudanar da bikin ranar Dimukradiyya a Najeriya ne tun shekarar 2002, haka kuma bayan da tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya hau mulki ya kuma ƙara wa ranar karfi bayan dawo da ita 12 ga watan Yuni.

To amma a cewar Mannir Ɗan Ali “Ga wasu daga cikin ƴan Najeriya da suke fama da tsadar rayuwa babu wani abu da dimokaradiyyar da ma mulkin farar hular suka tsinana musu, bare wannan rana ta June 12, domin ba abun da ke damunsu kenan ba''

Har yanzu dai yan Najeriya da dama na tafka muhawa game da matakin sauya ranar Dimokaradiyyar daga 29 ga watan Mayu zuwa 12 ga watan Yuni, inda wasu ke ganin cewa siyasa ce kawai a cikin lamarin, inji Dan Ali.

People are also reading