Home Back

Dala Ta Yi Muguwar Faɗuwa, Ta Dawo Ƙasa da N700 a Najeriya? Gaskiya Ta Bayyana

legit.ng 2024/5/18
  • Wani fitaccen mai amfani da X ya yi ikirarin cewa Dala ta ƙara karyewa zuwa N650 yayin da mutane suka fara sayar da Dalar da suka ɓoye
  • Legit Hausa ta tattaro cewa wannan ikirarin ya fara yawo ne yayin da Najeriya ke fama da matsin tattalin arziki
  • Wani shafi mai tsage gaskiya ya gudanar da bincike kan sahihancin wannan ikirari kuma ya wallafa rahotonsa ranar Jumu'a, 5 ga watan Afrilu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Yayin da Najeriya ke fama da hauhawar farashin kayayyaki, an fara yaɗa rahoton cewa Dala ta ƙara karyewa sosai a kasuwar canjin kuɗi.

A wani rahoto da ke yawo a soshiyal midiya, an yi ikirarin cewa farashin Dala ya dawo N850 da N650 a ranar 28 ga watan Maris, da ranar 1 ga watan Afrilu, 2024.

Gwamnan CBN, Cardoso.
Har yanzun Dala ta haura N1000 a kasuwar musayar kuɗi Hoto: Bloomberg, Central Bank of Nigeria Asali: Twitter

Yanayin yadda musayar kuɗi ke tafiya na Najeriya shi ne babbar alamar da ke nuna halin da tattalin arziƙin kasar ke ciki da kuma irin bunƙasa ko asakin haka da yake yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana ikirarin Dala ta faɗi a Najeriya

Wani mai amfani da shafukan sada zumunta, Honorabul Japhet Bodonyefa, ya wallafa saƙo a takaice a shafinsa na Facebook cewa:

"Dala ta sauka zuwa N850/1$."

Haka zalika, wani fitaccen ɗan soshiyal midiya, @PoojaMedia, ya yi ikirari a manhajar X cewa “Dala ta faɗo zuwa N650” yayin da ‘yan Najeriya ke rige-rigen sayar da dalolin da suka ɓoye.

Wannan iƙirari ya ja hankalin mutane akalla 1,200 da suka mayar da martani da ra'ayoyinsu, sama da mutum 900 suka tura wa abokansu yayin da 9,000 suka karanta.

Menene gaskiyar wannan ikirari?

Sakamakon yadda mutane suka raja'a a kan labarin, wani shafin tsage gaskiya, Dubawa ya yanke shawarar gudanar da bincike don tabbatar da gaskiya.

Bayan kammala bincike, Dubawa ta gano cewa bayanan da aka tattara a shafukan musayar kuɗi ya nuna har yanzu ana canjin Dala kan kuɗi sama da N1000.

Binciken ya tabbatar da cewa ikirarin da ke yawo a soshiyal midiya ba gaskiya bane, har yanzun Dala ta haura N1000 a kasuwar canji.

Naira: Yadda Dala ta faɗi a kasuwa

A wani rahoton kuma Daga ranar Laraba zuwa Juma’a, Dala ta rasa kimanin 5% a darajarta a kasuwannin bayan fagen ‘yan canji.

Masu canji sun tabbatar da kimar Naira ta karu da N70 a cikin ‘yan awanni, kimar kudin kasashen waje tana sauka.

Asali: Legit.ng

People are also reading