Home Back

Me rasa rinjayen Modi ke nufi ga Indiya?

bbc.com 2024/7/3
Narendra Modi looks thoughtful sitting at a table covered in flowers

Asalin hoton, Getty Images

  • Marubuci, Divya Arya
  • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Hindi

Narendra Modi na dab da kafa tarihin zama firaministan Indiya karo uku a jere.

Wani mataki da mutum ɗaya ne kawai ta taɓa kai wa a ƙasar, wato Jawaharlal Nehru, wanda ya jagoranci Indiya har tsawon shekara 16 bayan samun 'yancin kan ƙasar a 1947.

To sai dai nasarar da Mista Modi ya samu ta kasance tamkar abin nan da Hausawa ke cewa ''dakyar na tsira ya fi dakyar aka kamani''.

Jam'iyyarsa ta BJP ta rasa rinjaye a Lok Sabha, wato majalisar wakilan ƙasar, hakan na nufin dole ne ta nemi ƙulla kawance da wasu jam'iyyun domin kafa sabuwar gwamnati.

A tsawon lokacin mulkinsa, Mista Modi bai taɓa jagorantar gwamnatin kawance ba.

Jam'iyyar BJP ta samu kujeru 240, ƙasa da kujeru 303 da ta samu a zaɓen 2019.

Jam'iyyun adawa, ƙarƙashin jagorancin jam'iyyar CP sun ƙulla ƙawancen 'The Indian National Developmental Inclusive Alliance' (INDIA), inda suka haɗa karfi a lokacin zaɓen.

Ƙawancen ya samu nasara fiye da yadda aka yi tsammani, inda ya lashe kujerun majalisa 232.

Raguwar kujeru da jam'iyyar BJP ta samu zai sa ta samu raguwar ƙarfi a majalisar, lamarin da zai sa jam'iyyar ta fuskanci gagarumar adawa a majalisa.

Asalin hoton, Reuters

..
Bayanan hoto, Fastar Narendra Modi a shalkwatar jam'iyyar BJP a Gandhinagar

Jagoran ƙawancen, Rahul Gandhi, ya kira sakamakon zaɓen a matsayin gagarumin kaye ga firaministan, yana mai cewa ''ƙasarmu ta faɗa wa mista Modi cewa ba ma buƙatarka''.

Kamar dai a shekarar 2014 da 2019, jam'iyyar BJP ta yi yaƙin neman zaɓen 2024 ne da sunan Modi.

Hotunansa sun kasance a ko'ina a allunan tallace-tallace, inda 'yan takarar jam'iyyar suka yi ta haɗa hotunansu da nasa.

A lokutan gangamin yaƙin neman zaɓen, ya kira jama'a su zaɓe shi, inda ya ce zai cika alƙawuran da ya ɗaukar musu ciki har da ci gaba da bayar da tallafin walwala da gwamnatinsa ta shafe kusan shekara 10 tana bayarwa.

To sai dai ana kallon sakamakon zaɓen a matsayin wani gagarumin koma baya ga siyasar Modi.

Me ya sa BJP ta rasa kujeru?

“An karya tsafin Modi,” in ji Seema Chishti, editar jaridar Wire mai zaman kanta.

Wa'adin gwamnatin BJP na baya-bayan nan, ya fuskanci jerin zanga-zangar adawa da dokokin zaman ɗa ƙasa, waɗanda 'yan Indiya da dama ke kallo a matsayin masu nuna adawa da musulunci, da saɓa wa dokokin aikin noma da gwamnatin ta tilasta datakar da su.

An kuma zargi gwamnatin Mista Modi da tauye 'yancin 'yan jarida, da amfani da hukumomin bincike na ƙasa wajen cuzguna wa 'yan adawa.

A jawabinsa na farko da ya yi wa manema labarai bayan fitar da sakamakon zaɓen, shugaban kawancen jam'iyyun adawar, Raul Ghandhi riƙe da kundin tsarin mulkin ƙasar, ya ce talakawa da mutanen da ake nuna wa wariya sun yi yaƙi wajen ceto ƙasarsu bayan da suka zaɓi jam'iyyarsa.

Yogendra Yadav, mai sharhi kan harkokin siyasa ya kira rasa rinjayen Modi a matsayin ''Nasarar talakawa kan ƙusoshin gwamnati''.

To sai dai duk da rasa rinjayen da jam'iyyarsa ta yi, Mista Modi ya samu gagarumar tarba a lokacin da ya isa shalkwatar jam'iyyar domin bayyana godiyarsa ga magoya baya.

Magoya bayan jam'iyyar sun tarbe shi da furanni da tafi da kuma waƙoƙin nuna goyon baya.

Asalin hoton, Reuters

Indian Prime Minister Narendra Modi gestures as he arrives at Bharatiya Janata Party (BJP) headquarters in New Delhi, India
Bayanan hoto, Mita Modi lokacin da yake jinjina wa magoya bayansa a shalkwatar jam'iyyar BJP a New Delhi

Mista Modi bai nuna wata alamar damuwa a lokacin da yake gabatar da jawabi ga magoya bayansa ba.

A shekara mai zuwa ne zai cika shekara 75, shekarun da a baya ya taɓa cewa su ne shekarun da ya kamata ya ajiye aiki.

Narendra Modi ya kira nasararsa a matsayin gagaruma a duniya, tare da cewa ''za ta karfafa masa gwiwa wajen yin aiki tuƙuru''.

Kuma da alama zai fuskanci matsi yayin da zai jagoranci gwamnatin gamin gambiza.

Poornima Joshi, editar jaridar 'Hindu Business Line', ta ce a baya firaministan na amfani da rinjayen da jam'iyyarsa ke da shi wajen ɗaukar matakan da ya ga dama ciki har da korar manyan jami'an gwamnati.

Ta kara da ce “a yanzu dole wannan ɗabi'a ta kau.”

“Mista Modi ya rasa rinjayen da ke ba shi damar ɗaukar matakan da ya ga dama, kamar yadda ya yi a wa'adi biyun da suka gabata,” in ji Misis Joshi.

Me sakamakon ke nufi ga Musulman Indiya?

A lokacin da yake gangamin yaƙin neman zaɓen, Mista Modi ya sha fitowa ba tare da sakayawa ba, inda yake sukar musulman Indiya kusan miliyan 200, inda har ma yake danganta su da masu leken asiri.

A wani jawabi da ya taɓa gabatarwa ya bukaci mutane su yi zaɓe tsakanin ''zaɓar jihadi'' ko ''zaɓar mulkin gaskiya da adalci''.

Wata mata musulma ta shaida wa BBC cewa ''A yanzu babu wani sakayawa da ake yi, ƙarara ake fitowa fili ana sukarmu,''

Sakamakon zaɓen, musamman a garuruwan mabiya addinin Hindu, ya nuna rarrabuwar da aka samu tsakanin mabiya addinan Hindu da na Musulunci.

“A yaƙin neman zaɓenta, BJP ta alƙawarta ci gaba da ayyukan da ta faro a 2019, na goyon bayan harin soji a Pakistan da kuma sukar musulmi'', in ji Seema Chishti.

Ɗaya daga cikin manyan alƙawuran da BJP ta yi a lokacin yaƙin neman zaɓe shi ne samar da dokoki na kashin kai (UCC) ga duka Indiyawa, ba tare da la'akari da addini ba.

Asalin hoton, Reuters

Modi raises a hand while speaking at an election campaign rally, in New Delhi, India,
Bayanan hoto, Firaminista Modi ya sha sukar musulmai marasa rinjaye a lokutan yaƙin neman zaɓe.

Idan ana batun aure da saki da gado da riƙon yara, Indiya na da mabambantan dokoki ga mabambantan al'ummu, dangane da addini da aƙida.

Ƙabilu marasa rinjaye sun yi rajista da dokokin UCC, saboda fargabar da suke yi na yiwuwar tilasta sauya musu al'adunsu da yadda suke rayuwa.

A ƙoƙarinsa na mayar da dokokin UCC na ƙasa, A yanzu Mista Modi zai buƙaci tallafin abokan ƙawancensa domin tabbatar da dokar.

Kawo yanzu ba a san yadda sauran jam'iyyun ke kallon ƙudurin ba, kuma yayin da ba sabon abu ne ƙulla ƙawance domin kafa gwamnati a Indiya, a baya duka ƙawancen sun sha ƙarewa da rikici.

Yaya gwamnatin ƙawance ke shafar rayuwa a Indiya?

A wa'adin gwamnatin BJP mai ƙarewa, mafi yawan jam'iyyun adawa sun yi ƙorafin cewa ba sa iya jagorantar jihohin da suke mulki yadda ya kamata, sakamakon yadda BJP da ke jagorantar gwamnatin tarayya ke riƙe musu kuɗaɗensu.

Wannan ya haɗa da kuɗin yaƙi da aukuwar bala'o'i da na gine-ginen ababen more rayuwa da kuma na sauran ayyuka.

Nasarar da waɗannan jam'iyyu suka samu a zaɓen ka iya ƙara musu ƙarfin neman haƙƙoƙinsu daga gwamnatin tarayya domin yi wa al'umominsu ayyukan more rayuwa.

Yayin da take shirin fara wa'adin mulkinta na uku, BJP na iya neman samar da dokar ƙara ƙarfin iko kan kafafen yaɗa labarai ciki har da na zamani da aka jima ana suka a ƙasar.

A Indiya an sha zargin kafafen yaɗa labarai da tsananin biyayya ga gwamnati, ciki har da tsaron sukar manufofin gwmanatin.

To amma Mista Yadav na fatan cewa rasa rinjayen da BJP ta yi ka iya rage matsin lambar da take yi wa duk abin da ta sanya a gaba. ''Don haka kafafen yaɗa labarai ka iya samun 'yanci''.

People are also reading