Home Back

Bikin Sallah: Masu Hali A Tuna Da Fukara’u

leadership.ng 2024/6/26
Bikin Sallah: Masu Hali A Tuna Da Fukara’u

Idan Allah ya kai mu ranar Lahadi, 16 ga watan Yuni, 2024 za a yi bikin babbar sallah ta bana, watau 1445 Bayan Hijirah. Kamar yadda aka sani dai, babbar sallah lokaci ne da yake kunshe da ibadu da darussa da suke nuna sadaukarwa.

Kamar yadda kissa ta zo a cikin Alkur’ani mai girma, a lokacin bikin babbar sallah ana tuna sadaukarwar da Annabi Ibrahim (AS) ya yi da dansa, Annabi Isma’ilu (AS) bayan ya yi mafarkin cewa yana yanka shi. Haka nan shi ma Annabi Isma’ilu ya sadaukar da ransa domin biyayya ga mahaifinsa, inda ya amince ya gaskata mafarkin da ya yi domin daga Allah ne. Ita ma mahaifiyar Annabi Isma’ilu ta sadaukar da danta wanda har ya zamo silar samun ibadar jifar shaidan guda uku da ake yi na aikin Hajji, kamar yadda kissa ta nuna.

Allah ya dubi sadaukarwar da manyan bayinsa suka yi, da yake shi ne mafi girman ihsani, sai ya fanshe Annabi Ism’ilu da rago daga gidan aljanna, maimakon yanka dansa, sai Annabi Ibrahim ya yanka ragon.

Idan kuma aka dubi ibadar aikin Hajji, ita ma manuniya ce ga sadaukarwa. Duk isa da girman matsayin mutum, ba zai sa kayan da ya ga dama ba sai mayafi guda biyu, daya ya daura, daya kuma ya yafa sannan babu rufe kai.

Don haka, idan aka dubi darussan da suka kamata a koya a lokacin babbar sallah babu kamar sadaukarwa. Kuma wannan sadaukarwa babu lokacin da aka fi bukatarta a Nijeriya kamar a lokacin nan saboda yanayin halin matsi da ‘yan kasa ke ciki. Kodayake wasu gwamnatoci suna bakin kokarinsu wajen rage wa mutane radadin da suke sha, amma akwai bukatar masu hali su shigo cikin lamarin sosai, su sadaukar da wani sashe na dukiyarsu wajen faranta ran fukara’u wadanda su ba ma ta rago suke ba, ta abincin da za su ci suke kuma abincin ya yi tsada kwarai da gaske.

A kwanan nan, Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta bayyana cewa farashin shinkafa da garin kwaki da tumatir sun karu da kaso 141 a cikin shekara guda. Rahoton hukumar ya yi nuni da cewa farashin shinkafa ya karu da kaso 156, watau daga Naira 547 a 2023 zuwa Naira 1,399 a farkon 2024. A halin yanzu kuwa, farashin mudun shinkafa ta gida yana kaiwa tsakanin 1,900 zuwa 2,000.

Kazalika, farashin garin kwaki wanda shi ne mafi akasirin talakawa ke amfani da shi, ya karu da kaso 135, daga Naira 363 a watan Afrilun 2023 zuwa Naira 852 a shekarar 2024, cikin shekara guda kacal.

Hakazalika, farashin tumatir da aka fi amfani da shi a lokacin sallah, ya karu da kaso 17.9, daga Naira 960 zuwa Naira 1,123 a ma’auninsa, cikin ‘yan watannin baya, yanzu kuwa kwandon ya kai kusan Naira 150,000. Akalla ya karu da fiye da kashi 132 a cikin shekara guda.

Duka sauran nau’o’in abinci haka abin yake, babu sauki. A kullum farashin kaya kara hauhuwa yake yi. Shi ya sa abin ya tsallaka zuwa kan raguna wanda aka fi amfani da su a lokacin babbar sallah.

A wani bincike da wakilinmu ya gudanar a Kaduna, ragon da aka sayar a kan N100,000 a shekarar da ta gabata, yanzu yana kaiwa N200,000 zuwa N250,000. Matsakaitan raguna, a baya N120,000, yanzu suna tsakanin N400,000 zuwa N600,000. Manyan raguna, a da suna kan N700,000, amma yanzu sun haura zuwa tsakanin N900,000 da N1,000,000. Hatta ka fi zuru da ake cewa, sai mutum yana da Naira N70,000 zuwa N80,000.

Wasu masu sayar da dabbobin da aka ji ta bakinsu, sun ce an samu karin kudin ne daga masu kawo dabbobin da kuma tsadar abincinsu, wanda a yanzu farashinsa (buhu) ya kai Naira N20,000 zuwa Naira N25,000 idan aka kwatanta da Naira N10,000 a baya.

Bisa shari’ar addinin Musulunci, babu abin da Allah ya fi so a ranar babbar sallah kamar ibadar layya da ake yanka raguna. Rago aka fi so a layya saboda kamar yadda malamai suka yi bayani, dadin nama ake bi. Shi ya sa rago ya fi daraja, idan ba a samu ba sai a yi da tunkiya, ita kuma ta fi bunsuru daraja a layya, shi kuma ya fi akuya, ita kuma ta fi bajimin sa, shi kuma ya fi saniya, ita kuma saniya ta fi namijin rakumi inda shi kuma ya fi rakuma mace. Amma a ibadar hadaya na mahajjata, an fi son yawan nama. Shi ya sa rakumi ya fi daraja kuma a nan.

To yanzu, duk a cikin wadannan dabbobin, dabbar da aka fi so a yi layyar da ita, rago shi ne mai saukin kudi a cikinsu, amma kuma ba ta shi ake ba saboda tsananin kuncin rayuwar da ake ciki. A wannan makon, Hukumar Kula da Wadatar Abinci da Aikin Gona ta Duniya, ta bayyana cewa matsananciyar yunwa na barazana ga mutum akalla miliyan 4.8 a yankin Arewa Maso Gabas kawai. A yanki daya kenan daga cikin manyan yankunan siyasa shida na kasar nan, kenan idan aka duba sauran yankunan musamman arewa maso yamma wanda shi ma yake fama da barnar masu sace-sacen mutane suna garkuwa da su, miliyan nawa za a samu.

Shi ya sa, ya kamata masu hannu da shuni, su dubi girman Mahaliccin da ya dora su kalifofi a kan dukiyar da suke amfana da ita, su taimaki rayuwar talakawa musamman a wannan lokaci na babbar sallah. Mun tabbata, babu wani mai imani da zai so, shi a gidansa an yanka raguna, an yi abinci na kasaita, amma ga wani talaka can shi ko girki ba a dora ba ballantana a yi maganar yanka rago.

Har ila yau, ba sai mutum ya cika ya tumbatsa da dukiya ba ne zai iya taimako, kowa ya yi iya gwargwadon yadda zai iya, da haka za a samu saukin wannan kuncin rayuwa da fukara’u ke ciki. Kar a manta, duk abin da aka yi tamkar bashi ne aka ba Allah. Sannan Manzon Allah (SAW) ya ce, “Allah yana cikin taimakon bawa matukar bawa yana cikin taimakon dan uwansa”.

People are also reading