Home Back

Da Gaske Arsenal Ta Kawo Karfi?

leadership.ng 2024/5/18
Arsenal Ta Sake Tabbatar Da Cancantar Lashe Firimiya

A shekarun baya idan ana maganar kungiyoyin da za su iya lashe gasar firimiyar Ingila kungiyar Arsenal ba ta shigowa saboda rashin kokarin kungiyar da kuma rashin tsarin shugabanci a lokacin, wanda har ta kai kungiyar ba ta iya zuwa gasar cin kofin Zakarun Turai a jere.

Amma a yanzu ya zama dole ka saka Arsenal a cikin jerin kungiyoyin da za su iya lashe gasar, ko ba don komai ba, domin irin kokarin kungiyar a cikin shekaru biyu, na zamowa daya daga cikin manyan kungiyoyin da suke takarar lashe firimiyar Ingila.

A ranar Lahadi kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta je ta doke kungiyar Tottenham da ci 3-2 a wasan mako na 35 a gasar Premier da suka kara a wasan hamayya kuma Arsenal ce ta fara zura kwallaye uku a raga ta hannun Pierre-Emile Hojbjerg, wanda ya ci gida a minti na 15 da fara wasa sai dan wasa Bukayo Saka da ya zura kwallo ta biyu sai kuma Kai Habertz da ya zura ta uku.

Haka kuma dan wasa Saka ya zama dan wasan tawagar Ingila da ya ci Tottenham gida da waje a Premier League a kaka daya, tun bayan bajintar Ian Wright ya yi a shekarar 1993 zuwa 1994.

Amma daga baya Tottenham ta zare kwallaye biyu ta hannun Cristian Romero da Heung-min Son a bugun fenariti kuma sakamakon wasan ya nuna karo biyu a jere Arsenal na zuwa ta na cin Tottenham tun bayan Satumbar 1988 da ta yi nasara uku, karkashin George Graham.

Kafin nan wasa biyu Arsenal ta ci a gidan Tottenham daga wasanni 17 da ta kai ziyara a Premier da canjaras shida aka doke ta tara daga ciki wanda hakan ya nuna irin bajintar da Arsenal din tayi cikin ‘yan shekarun nan.

Wasan na ranar Lahadi shi ne wasa na 100 da Mikel Arteta ya ci a Premier League a karawa ta 169 da ya ja ragamar Arsenal a babbar gasar firimiya ta Ingila kuma cikin wasannin ya yi canjaras 27 aka doke shi 42 da cin kwallo 321, aka zura wa Arsenal 179.
Bayan da Arsenal ta doke Tottenham ta ci gaba da zama ta daya a kan teburin Premier League da maki 80, yayin da Manchester City ce ta biyu mai maki 79, mai kwantan wasa daya sai kungiyar Liberpool, wadda ta tashi 2-2 da West Ham United tana ta ukun teburi da maki 75.

Ita ma Manchester City ta ci gaba da zama ne a mataki na biyu a teburin Premier League, bayan da ta je ta doke Nottingham Forest 2-0 a wasan mako na 35 ranar Laha-din da yamma.

Dan wasa Josko Gbardiol ne ya fara zura kwallo a raga a minti na 32, sannan Erling Halland ya ci ta biyu saura minti 19 a tashi daga wasan kuma kwallo ta 21 da Halland ya zura a raga a wasa na 25 da ya buga a bana kenan a babbar gasar firimiya ta Ingila.

Rabon da Haaland ya ci kwallo a Manchester City tun ranar 13 ga Afirilu a karawar da Manchester City ta lallasa kungiyar Luton Town 5-1 a gasar ta Premier League kuma wannan shi ne wasa na 300 da Pep Guardiola ya ja ragamar Manchester City a Premier da yin nasara 221 da canjaras 41 aka doke shi 38 sannan ya ci kwallo 741 aka zura masa 247 a raga.

Guardiola dan kasar Spain mai shekara 53 a duniya ya koma Manchester City ranar 1 ga watan Yulin 2016, yanzu yana kakar wasa ta takwas da kungiyar sannan ya kuma fara jan ragamar karawar Premier League ranar 13 ga Agustan 2016, wanda ya doke Sunderland 2-1 a Etihad.

Haaland tsohon dan wasan Borussia Dortmund wanda ya yi jinya, bai yi wa Manchester City wasan FA Cup da ta doke Chelsea ta kai zagayen karshe ranar 20 ga Afirilu ba.

Haka kuma bai samu buga wa Manchester City wasan da ta je ta dura kwallaye 4-0 a ragar Brighton ba a Premier League ranar 25 ga watan Afirilu duka saboda ciwon da yake fama da shi.

Wasannin da ke gaban Manchester City da na Arsenal:
Man City: 4 Mayu a gida da Wolbes; 11 Mayu zuwa gidan Fulham; 14 Mayu zuwa gidan Tottenham; 19 Mayu a gida da West Ham. Arsenal: 4 Mayu a gida da Bournemouth; 12 Mayu zuwa gidan Man Utd; 19. Mayu a gida da Eberton.

People are also reading