Home Back

NOMA TUSHEN ARZIKI: Gwamna Namadi zai raba Naira biliyan 3.5 na tallafin korona ga manoma 30,000

premiumtimesng.com 2024/8/24
RANGADIN DUBA NOMAN SHINKAFA A JIGAWA: Muna sa ran samun tan miliyan 1.6 na shinkafa cikin wannan shekarar – Gwamna Namadi

Manoma aƙalla 30,000 waɗanda suka samu tawayar noma a lokacin ɓarkewar cutar korona, za su samu tallafin Naira biliyan 3.5 daga Gwamnatin Jihar Jigawa.

An bayyana wa manema labarai amincewar da gwamnatin jihar ta yi na a raba tallafin na Naira biliyan 3.5 bayan kammala taron Majalisar Zartaswa na baya-bayan nan da ya gudana.

Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Jigawa, ya bayyana wa manema labarai cewa maƙasudin tallafin shi ne domin a taimaka wa marasa galihu da talakawa a ƙarƙashin shirin noma na FADAMA, Shiri na 4 da na 5, kamar Ma’aikatar Ayyukan Noma da Albarkatun Ƙasa ta gabatar, a matsayin wani shiri na ƙasa wadatar abinci a jihar.

Ya ce, Gwamnati tare da Bankin Duniya na ƙoƙarin ganin cewa sun tabbatar manoma sun farfaɗo domin samun noma abincin dogaro a rayuwar su.”

Dama a baya an ruwaito cewa Gwamna Umar Namadi ya yi alƙawarin tallafa wa talakawa da marasa galihu 30,000 kafin ƙarshen shekarar 2024.

Kwamishinan ya jaddada muhimmancin tallafa wa manoman karkara domin farfaɗowa daga tawayar da suka fuskanta a lokacin ɓarkewar cutar korona.

Gwamna Namadi ya ce tsare-tsaren gwamnatin sa ba su tsaya kan magance matsalolin da aka fuskanta lokacin korona kaɗai ba, za su taimaka wajen ɗorewa da ci gaban bunƙasar tattalin arziki a cikin jihar ta fuskar bunƙasa harkokin noma.

An tallafa wa manoman karkara da kayan noma da domin bunƙasa noma da samar da abinci.

People are also reading