Home Back

Yajin Aiki: Likitoci a Kano Sun Watsawa Kungiyar NLC Kasa a Ido

legit.ng 2024/6/29
  • Kungiyar likitoci ta kasa NMA reshen jihar Kano ta janye jikinta daga yajin aikin da kungiyoyin kwadago a Najeriya suka fara a Litinin din nan
  • Kungiyar kwadago ta kasa NLC da takwararta ta TUC na bukatar gwamnatin kasar nan ta amince da biyan ma’aikata N494,000 a matsayin mafi karancin albashi
  • Rashin cimma matsaya ne ya sa kungiyar ta kira gangamin yajin aikin gama gari, amma NMA ta bayyana cewa dukkanin mambobinta su fito bakin aiki domin ba su a cikin NLC

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano- Kungiyar likitoci ta kasa (NMA) reshen Kano ta umarci mambobinta su fito aiki a asibitocin dake jihar domin ba za su shiga yajin aiki ba.

Kungiyar ta umarci ‘ya’yanta su bijirewa yajin aikin sai baba ta gani da kungiyoyin kwadago suka tsunduma bayan gaza cimma matsaya kan mafi karancin albashi da gwamnati.

Likitoci
Kungiyar likitoci a Kano ta bijirewa yajin aiki (An yi amfani da hoton nan saboda misali) Hoto: Shannon Fagan Asali: Getty Images

Daily Trust ta tattaro cewa yajin aikin da aka fara a safiyar yau ya shafi bangarori da dama ciki har da sufurin jirgin sama, bankuna, asibitoci da ma’aikatun gwamnati.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me yasa NMA kin shiga yajin aiki?

A yau ne aka fara yajin aikin gama gari kuma na sai baba-ta-gani a fadin Najeriya kamar yadda Nigerian Tribune ta wallafa, sai dai kungiyar likitoci reshen jihar Kano ta ce ba da ita ba.

Sakataren kungiyar a Kano, Dr Abdurrahman Ali, ya ce su kungiyar kwararrun ma’aikata ne kuma babu su cikin mambobin kungiyar kwadago ta kasa.

Ya ce za a samu ma’aikatansu baki daya a bakin aiki, duk da cewa akwai yiwuwar a samu wasu ma’aikatan lafiya da ba mambobinsu ba basa bakin aiki.

Yajin aiki: An rufe tashar wutar lantarki

A baya mun kawo muku labarin yadda kungiyar kwadago ta kasa ta garkame kamfanin kula da rarraba hasken wutar lantarki na kasa a yunkurin tabbatar da kowa ya shiga yajin aiki.

Kungiyoyinkwadago a Najeriya sun tsunduma yajin aikin sai baba ta gani saboda biris da bukatar biyan mafi karancin albashin N494,000 da gwamnatin tarayya ta yi.

Asali: Legit.ng

People are also reading