Home Back

Isra’ila Na Ci Gaba Da Take Dokokin Duniya A Gaza – Majalisar Dinkin Duniya

leadership.ng 6 days ago
Isra’ila Na Ci Gaba Da Take Dokokin Duniya A Gaza – Majalisar Dinkin Duniya

Hukumar kare hakkin bil’Adama ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce tana ganin Isra’ila na ci gaba da saba dokokin duniya a ruwan bama-bamai da take yi a Gaza.

Hukumar ta yi nazari a kan wasu hare-haren bam shida da Isra’ilar ta kai a shekarar da ta wuce, wadanda ta kai gidajen jama’a da makaranta da sansanonin an gudun hijira da kuma wata kasuwa.

Ta ce, manyan makaman da aka yi amfani da su ba za su iya tantance tsakanin farar hula da mayaka ba, saboda haka babu dalilin yin amfani da su a wuraren.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce ta tabbatar da mutuwar mutum 218 a hare-haren amma tana ganin yawan ma ya fi haka.

Babban Jami’in Kula da Hakkin Dan’Adam na Majalisar, Bolker Turk, ya ce hare-haren bom na Isra’ila ka iya zama laifukan cin zarafin bil’Adama.

Al’ummar Zirin Gaza na cikin mawuyacin hali na mummunar illa ga lafiya da kuma muhallinsu saboda yakin da Isra’ila ke yi da Hamas ya tilasta musu zama cikin kazanta.

Asmahan al-Masri, wacce ta yi gudun hijira daga Beit Hanoun, yanzu tana zaune a Khan Younis, ta bayyana halin da ake ciki a Gaza a matsayin kisan mummuke, inda ta koka da cututtukan da jikokinta ke fama da su, wadanda suka hada da karzuwa.

A cikin wata takwas da ya gabata, fiye da tan 330,400 na bola aka tara a Gaza, kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyin agaji suka bayyana.

Mutum 16 na dangin Masri na cunkushe a cikin wani tanti kusa da jami’ar al-Aksa, kewaye da kudaje da karnuka da warin sharar da ta rube.

Mawuyacin hali ya tilasta wa mutane da yawa, kamar Mohamed, kalen abinci da sauran tarkace domin sayarwa don su rayu.

Sama da mutum miliyan daya da suka tsere daga harin da sojojin Isra’ila suka kai a Rafah yanzu haka suna zaune a yankunan da suka koma wurin tara shara na wucin-gadi.

Ali Nasser, wanda kwanan nan ya koma sansanin jami’ar al-Aksa daga Rafah, ya bayyana irin halin da suke ciki da suka hada da larurar amai da gudawa, da kuma karzuwa saboda rashin kyawun rayuwa.

Shekaru da dama da Isra’ila da Masar suka yi na killace yankin ya haifar da cikas ga ayyukan yau da kullum kamar zubar da shara a Gaza.

Tun bayan harin da Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba, sojojin Isra’ila suka toshe hanyoyin shiga manyan wuraren da ake zubar da shara a Gaza, lamarin da ya ta’azzara rikicin.

A cewar Sam Rose, darektan tsare-tsare na hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Falasdinawa UNRWA, yanayin kula da shara a Gaza ya tabarbare matuka.

Hotunan shafukan intanet da binciken da BBC Berify ta yi sun nuna yadda ake samun yawan zubar da shara barkatai, yayin da mutane ke tserewa zuwa garuruwa da birane daban-daban.

Yawancin wuraren kula da ruwa da bahaya sun lalace.

People are also reading