Home Back

Farashin Man Fetur Ya Ragu a Gidajen Mai Yayin da Dala Ta Ƙara Karyewa a Najeriya

legit.ng 2024/5/20
  • Wasu daga cikin gidajen mai a Najeriya sun rage farashin litar man fetur yayin da Naira ke ƙara farfaɗowa kan Dala a kasuwar canji
  • Saukar farashin fetur ka iya rage tsadar kudin sufuri da kuma rage nauye-nauyen da suka yi wa magidanta yawa a faɗin ƙasar nan
  • A. halin yanzun, kuɗin Najeriya ya ƙara daraja mafi girma kan Dalar Amurka a watanni bakwai da suka gabata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Farashin man PMS wanda aka sani da fetur ya ragu daga N640 da N660 da ake sayarwa a a ƴan makonnin da suka shige zuwa N620 kan kowace lita a wasu wurare a jihar Legas.

Wannan sauki da aka samu a farashin litar Fetur ba zai rasa nasaba da tashin darajar Naira kan Dalar Amurka da ake ta samu a ƴan kwanakin nan.

Gidan mai.
Sauƙi na kara samuwa yayin da farashin fetur ya kara sauka a gidajen mai Hoto: Benson Ibeaubuchi Asali: Getty Images

Yayin da Legit Hausa ta ziyarci wasu gidajen mai mallakin kamfanin mai na ƙasa (NNPCL) ta gano cewa farashim fetur ya sauka zuwa N580 kan kowace lita.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Duk da har kawo yanzu NNPCL bai sanar da ci gaban a hukumance ba amma raguwar farashin fetur alama ce ta samun sauƙi yayin da ake fama da tsadar rayuwa.

Yadda farashin ya sauka

Da yake tsokaci kan lamarin, wani manajan gidan mai da ya rage lita zuwa N620 a Legas, Kunle Ademola, ya ce farashin da suke karɓo man ne ya sa suka rage daga N650 zuwa N620.

"Kwanaki kaɗan da suka wuce sun kulle gidan mai amma yanzu kaya sun iso. Duk da wasu gidajen mai da ke kusa da mu suna sayarwa a kan N650, mun rage na mu zuwa farashin da bai ka haka ba.
"Mun sauke farashin lita ne saboda mun karɓi sabon kaya kan farashin da bai kai wanda muka biya a baya ba," in ji manajan.

Farashin Naira da fetur

A wata hira, tsohon shugaban kungiyar ƴan kasuwar mai (IPMAN), Chinedu Okoronkwo, ya yi bayanin alaƙar musayar kuɗin Najeriya da farashin man fetur.

Ya ce:

"Ƴan Najeriya sun san cewa an cire tallafi, don haka mun zo wani zamani da yanayin kasuwa ne ke taka rawa. Matukar Dala za ya kaɗa tsada, fatashin fetur zai ci gaba da ƙaruwa."
"Haka abun yake idan kuma Naira ce ta ƙara daraja, ma'ana fetur zai sauko kenan."

Daga farkon makon nan zuwa, Naira ta tashi a kasuwar musayar kuɗi inɗa ta kusa dawo $1/N1000.

Tinubu ya kaddamar da tsari

A wani rahoton Bola Ahmed Tinubu ya kaddamar da sabon tsarin aiki wanda zai rage asarar makudan kuɗin shiga a Najeriya duk shekara.

Shugaban ƙasar ya ce Najeriya za ta ceto $4bn a kowace shekara ta hanyar rage ayyukan ofis da toshe hanyoyin cin hanci da rashawa.

Asali: Legit.ng

People are also reading