Home Back

Mummunar Gobara Ta Tashi a Kwalejin Fasaha Ta Jihar Kano, an Tafka Asara Mai Yawa

legit.ng 2024/7/4
  • Wata mummunar gobara ta tashi a kwalejin fasaha ta jihar Kano da safiyar yau Talata, inda ta jawo asarar dukiya mai tarin yawa
  • An ruwaito cewa gobarar ta babbake kafatanin sashen koyon Arts and Industrial na kwalejin da ke a bangaren koyon fasaha na kwalejin
  • Kakakin hukumar kashe gobara na Kano, Saminu Abdullahi wanda ya tabbatar da lamarin ya ce har yanzu ba a gano musabbabin wutar ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kano - An tashi cikin wani mummunan yanayi a jihar Kano bayan da wata gobara ta babbake ilahirin bangaren koyon ilimin fasaha da ke a cikin kwalejin fasaha ta Kano.

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano
Gobara ta kone ajujuwa da ofisoshi a kwalejin fasaha ta Kano. Hoto: @Fedfireng Asali: Facebook

Rahotanni sun bayyana cewa gobarar ta babbake kafatanin sashen koyon Arts and Industrial na kwalejin a safiyar yau Talata.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Yusif Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gobara ta babbake kwalejin Kano

Saminu Abdullahi wanda ya ce har yanzu ba a gano musabbabin tashin gobarar ba ya ce gobarar ta lakume dukiya mai yawa amma ba a kammala tantance wa ba.

A cewarsa hukumar ta samu kiran gaggawa daga wani Faisal Dauda wanda ya ba da rahoton cewa an samu tashin gobara a kwalejin fasahar.

Mista Saminu ya bayyana cewa ginin mai dauke da ajujuwa tara da ofisoshi shida ya lalace gaba daya.

Kakakin hukumar kashe gobarar ya yi nuni da cewa ba a samu asarar rayuka ba, kuma ana ci gaba da binciken musabbabin tashin gobarar.

Abba zai biya Doguwa diyyar N25m

A wani labarin, mun ruwaito cewa wata babbar kotu da ke jihar Kano ta umarci gwamnatin jihar Kano da ta biya Alhassan Ado Doguwa diyyar Naira miliyan 25.

A cikin takardar hukuncin da kotun ta yanke mai lamba FHC/ABJ/ABJ/CS/714/2019, an wanke Hon. Ado Doguwa daga zargin kisan kai.

Wannan na zuwa ne bayan da gwamnatin NNPP a Kano ta gurfanar da Doguwa a gaban kotu ne kan zargin mutuwar mutane akalla 15 a zaben zaben shugaban kasa na 2023.

Asali: Legit.ng

People are also reading