Home Back

Sojojin Sun Samu Galaba Kan Ƴan Bindiga, an Kama Masu Safarar Makamai a Arewa

legit.ng 5 days ago
  • Sojojin Najeriya sun samu nasarar cafke 'yan bindiga da kuma wadanda suke kai wa 'yan bindigar makamai a jihohi biyu na Arewa
  • Kakakin rundunar soji da ke atisayen OPSH, Manjo Samson Zhakom ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Jos, jihar Filato
  • Manjo Samsom ya ce sojojin sun kwato bindigogi da dama da suka hada da AK47 da kuma tarin alburusai a yayin samamen

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jos, jihar Filato - Dakarun sojojin Najeriya da ke atisayen OPSH da na runduna ta 3 sun yi galaba kan 'yan bindiga da masu kai masu makamai a johohin Filato da Kaduna.

A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar OPSH, Manjo Samson Zhakom ya fitar a ranar Litinin, ya ce dakarun hadin guiwar ne suka cafke wadanda ake zargin.

Sojoji sun yi magana kan kama 'yan bindiga a Arewa
Sojoji sun cafke 'yan bindiga da masu kai masu makamai a Filato da Kaduna. Hoto: @HQNigerianArmy Asali: Facebook

Manjo Zhakom ya kara da cewa dakarun sojojin sun kwato makamai da alburusai da dama yayin samamen da suka dau mako suna kai wa, in ji rahoton The Cable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji sun kai samame dajin Filato

Sanarwar ta ce:

"A ranar 21 ga watan Yuni, sojoji sun kai same mabuyar 'yan bindiga da ke dajin Pandam, a Qua'anpan, jihar Filato.
"Yayin kai samamen, dakarun sun kwato bindigogi 3 kirar AK47, gidan harsashi 5 na AK47 da harsasai 75 masu tsayin 7.6mm.
"Haka zalika, a ranar 21 ga Yuni, sojoji da sauran jami'an tsaro sun kama wani mai kai wa 'yan bindiga makamai a hanyar Jos-Abuja, a Riyam, jihar Filato."

Samamen sojoji ya kai har zuwa Kaduna

Jaridar Vanguard ta ruwaito sanarwar ta kara da cewa:

"Bayan kama mai safarar makaman ne, dakarun suka bibiyi wanda zai sayarwa bindigogi 35 kirar AK47, wanda shi ma aka kama shi a jihar Kano.
"Bayanan da aka samu daga wadanda aka kama ya taimakawa dakarun wajen cafke manyan masu dillancin makamai ga 'yan bindiga Manchock, Kaura, da ke jihar Kaduna.
"An yi nasarar kama shi ne lokacin da ya ke kokarin kulla harkallar safarar bindigogi 35 ga wanda aka kama a Jos domin kai wa ƴan bindiga a Zamfara."

An kama makisan Birgediya Janar a Abuja

A wani labarin, mun ruwaito rundunar 'yan sandan Abuja ta ce ta samu nasarar kama mutum hudu da ake zargin sun kashe Manjo Janar Uwem Udokwere (mai ritaya) a Abuja.

Kwamishinan'yan sandan Abuja, Benneth Igweh ya ce wadanda ake zargin sun kashe tsohon sojan ne a gidansa a ranar Asabar, kuma har yanzu ana farautar mutum biyu.

Asali: Legit.ng

People are also reading