Home Back

Masu tallar kayan ƙawa sun bai wa Falasɗinawa tallafin dala miliyan ɗaya

bbc.com 2024/6/18

Asalin hoton, Getty Images

...
Bayanan hoto, Bella Hadid (dama) da Gigi Hadid (hagu), two American supermodel sisters
  • Marubuci, Guy Lambert
  • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC
  • Mintuna 7 da suka wuce

Shahararrun mata ƴan Amurka masu tallar kayan ƙawa, Bella da Gigi Hadid sun bai wa Falasɗinawa tallafin kuɗi dalar Amurka miliyan ɗaya.

Ɗaya daga cikin lauyoyin Bella Hadid ya ce an tsara yadda za a raba kuɗin daidai-wa-daida tsakanin hukumomin bayar da agaji huɗu waɗanda ke aikin tallafa wa yara da iyalan da yaƙin Gaza a shafa.

Matan biyu waɗanda mahaifinsu, Muhammad Anwar Hadid ɗan kasuwa ne mai harkar gine-gine, sun daɗe suna nuna goyon bayansu ga Falasɗinawa tun bayan ɓarkewar yaƙi a yankin.

A wani bayani da ta wallafa a shafinta na instagram a watan Mayu, Bella ta ce: "Na kaɗu ƙwarai da rashin tausayin da ƙasashen duniya ke nunawa game da kisan Falasɗinawa da ake yi."

Asalin hoton, Getty Images

...
Bayanan hoto, Kayan da Bella Hadid ta sanya mai launin ja da fari mai kama da mayafin da Larabawa ke yafawa domin nuna goyon baya ga Falasɗinawa

Bayan harin da Hamas ta kai kan Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba, Gigi ta rubuta a shafinta na Instagram cewa: "Ina jajanta wa duk waɗanda wannan mummunan lamari ya shafa, wanda ya ke haifar da kisan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba a kowace rana, waɗanda mafi yawancin su yara ne."

"Fafutikar da Falasɗinawa ke yi a ƙarƙashin mamaye lamari ne da ke sosa min zuciya, abu ne da nake jin cewa nauyi ne a kaina a kowace rana."

"Duk da cewa ina fatan ganin cewa Falasɗinawa sun samu ƴanci, hakan ba yana nufin a cutar da Yahudawa ba."

Hukumomin bayar da tallafi wadanda aka bai wa kuɗaɗen da Bella da Gigi suka bayar su ne: Asusun Yaran Falasɗinawa, Hukumar bayar da agajin abinci ta World Central Kitchedn, Hukumar samar da tallafi da ayyuka ga Falasɗinawa ta MDD UNRWA), da kuma Hukumar tallafa wa Falasɗinawa ta Palestine Healing.

Wadannan hukumomi na samar da gudumawar abinci da kayan kiwon lafiya da shawarwari ga Falasɗinawa waɗanda rikici ya tarwatsa musamman waɗanda suke a a Gaza.

A ranar Juma'a shugaban Amurka, Joe Biden ya yi kira ga Hamas da ta amince da tayin Isra'ila na dakatar da yaƙi a Gaza, inda ya ce "lokaci ya zo da za a kawo ƙarshen wannan yaƙi."

Rikici ya ɓarke a Gaza ne bayan da mayaƙan Hamas suka kai wani gagarumin hari kan kudancin Isra'ila, lamarin da ya kashe kimanin mutum 1,200 yayin da aka yi garkuwa da wasu mutanen 252.

Bayan nan ne Isra'ila ta ƙaddamar da hare-hare kan Gaza.

Hukumomin Hamas a Gaza sun bayyana cewa kimanin mutum 36,000 ne aka kashe tun bayan ɓarkewar wannan rikicin.

People are also reading